Game Da Mu

Daily Feeds kafar yada labarai ce ta Internet dake Najeriya wacce ke da babban ofishinta a birnin tarayya Abuja- kuma an samar da ita ne domin girmawa tare da fito da al’adu da kare kimar Najeriya a idon duniya.

Wannan kafa ta yada labarai, Daily Feeds, rukunin kwarraru da gogaggun ‘yan jarida ne suka ƙirƙire ta, wadanda suke da kwadayin bunkasa tsarin dimukuradiyya da zaman lafiya da kuma bada gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ta hanyar amfani da tsarin da duniya ke kai wajen yada rahotanni da shirye shirye, kamfanin Daily Feeds zai taka rawa wajen kare hakkin mazauna kasa da yaki da cin hanci da rashawa da yaki da yada labaran karya da kuma dakile dabi’ar yada labaran tada hargistsi.

Haka kuma, mamallaka wannan kafa a ko da yaushe zasu taka muhimmiyar rawa wajen bada shawarar gudanar da shugabanci nagari da zai bunkasa rayuwar ‘yan Najeriya, ta hanyar faɗakarwa da ilimantar da masu rike da madafun iko da Malamai da matasa kan abinda yafi dacewa ga kowa.

Baya ga haka, kamfanin Daily Feeds za a iya tuntuɓarsa akan abibda ya shafi ayyukan tattara labarai da tallace-tallace da sauran ayyukan da suka shafi kafar yada labarai.