Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaKungiyar Tinubu Support Group Tayi Rabon Tallafi ga Kungiyoyi

Kungiyar Tinubu Support Group Tayi Rabon Tallafi ga Kungiyoyi

Date:

Kungiyar Tinubu Support Group Tayi Rabon Tallafi ga Kungiyoyi

Gamayyar Kungiyoyin dake goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wato Tinubu support Group (TSG), tayi rabon tallafin dogaro dakai ga wasu daga cikin ‘yan Kungiyoyin magoya bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gamayyar Kungiyoyin karkashin jagorancin Darakta Janar na hukumar kula da nagartar ayyuka (NPC) Dr Baffa Babba Dan’Agundi, ta raba baburan hawa da babura masu kafa uku (Adaidaita Sahu) da babura masu kafa uku na daukar kaya, da kekunan dinki, da karamar motar daukar kaya, da injinan markade, da kayan kiwon kifi dana kaji da shanu harma da kayan abinci.

Dayake jawabi yayin bikin daya gudana a cibiyar yakin neman zaben BOLA TINUBU SUPPORT GROUP dake kan titin Audu Bako, Dr Baffa Babba Dan’Agundi ya godewa Dan majalisar tarayya mai wakiltar Bichi kuma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Engr Abba Kabir Bichi wanda yace shine ya samar da wadannan kayayyaki da aka rabawa ‘ya’yan wadannan Kungiyoyi.

Dr Dan’Agundi ya kuma godewa Gwamnan jihar Kano Alh Abba Kabir Yusuf wanda yace yayi alkawarin tallafawa wadannan Kungiyoyi nan da bayan Sallah.
Kungiyoyi daga jihohi bakwai na Arewa maso yamma ne suka amfana da wannan tallafi.

A jawabinta tunda fari, kwamishina a hukumar kula da rabon arzikin kasa Mrs Ginika Toh, ta yabawa Dr Baffa Babba Dan’Agundi bisa irin jajircewar da yake wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu inda tayi fatan sauran ‘yan siyasa zasuyi koyi dashi.

Taron ya samu halartar jagoran jam’iyyar APC na karamar hukumar Birni tsohon Kwamishina Hon Muntari Ishaq da tsohon Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Hon Garba Yusuf Abubakar da mai baiwa gwamna shawara kan tallafi da jinkai Hon Alhajiji Kankarofi da sauran manyan baki daga sassan kasarnan daban daban.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories