Thursday, April 30, 2026
HomeBincikeKotu Ta Dage Zaman Shari’ar Kisan Jami’in Civil Defense

Kotu Ta Dage Zaman Shari’ar Kisan Jami’in Civil Defense

Date:

Kotu Ta Dage Zaman Shari’ar Kisan Jami’in Civil Defense

Kotun Majistare mai lamba huɗu, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Rakiya Lami Sani, ta sake dage ci gaba da sauraron shari’ar kisan jami’in hukumar Civil Defense, Abdurrauf Ali Ahmad Sharifai, sakamakon rashin lafiyar lauyan masu gabatar da ƙara.

Kotun ta dage sauraron shari’ar zargin kisan kai da ake yi wa Aminu Isa, Ayuba Idris, Yunusa Sunusi, Umar Sulaiman da Isuhu Hassan, waɗanda ake zargi da kashe jami’in tsaro na Civil Defense a ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

Mai Shari’a Rakiya Lami Sani ta sanya ranar Litinin, 23 ga watan Maris, 2026, domin karɓar shawarwarin shari’a daga ofishin Babban Lauyan Gwamnati da kuma Kwamishinan Shari’a na jihar kan lamarin.

Idan Za’a  iya tunawa, an kashe Abdurrauf Ali Ahmad Sharifai ne  ta hanyar kisan gilla da  wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sukayi masa, yayin da yake kan gudanar da aikinsa ranar daya ga watan Janerun 2026.

Bayan zurfafa bincike, rundunar ‘yansanda tare da haɗin gwiwar hukumar Civil Defense sun samu nasarar kama mutane biyar, inda aka gurfanar da su a gaban kotu a ranar 14 ga watan Janairu, 2026.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories