A yadda tsarin kasashe ko jihohi yake a wannan zamani, tsaro baya samuwa ta hanyar karfi kawai face ta hanyar tsare tsare, tsarin gudanarwa mai kyau, kyakyawan tunani dakuma tabbacin gudanuwa.
A wannan nahiyar ta mu ta Afirka, da ma sauran yankuna a duniya baki ɗaya, irin wannan tsari na zamani yana ƙara zama muhimmi wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
A wannan fanni ne aka yi nazari game da irin kokarin aikin da Mataimakin Kwanturola-Janar na Kwastam (DCG) Isah Umar Gusau mai ritaya yayi a lokacin da yake gudanar da aikinsa, inda ya samar da jadawali mai nagarta da kuma shugabanci na gari musamman a fannin tsaron kasa, bunkasa kasuwanci da inganta tsarin adana kuɗaɗe.
A tsawon lokacin da ya dauka yana aiki a hukumar hana fasa ƙwabri ta kasa ba kawai za’a ayyana shi bane saboda muƙama da ya riƙe, wajibi ne a haɗa da tsare tsaren da ya inganta wajen gudanar da aiki da domin bunkasa hukumar. Wannan shine zayyanannen labarin ƙwarewa a fannin shugabanci wanda ya wuce tursasawa ko kuma kama-karya.
Ga duk wanda ya san DCG Isah Gusau, nagartarsa wurin sanin makamar aiki da kuwa ƙwarewa ba abin ayi musu akai bace. Nazari akan ma’aikata irin DCG Isah Gusau, yana ƙara tabbatar da cewa ba’a gabatar da nagarta a matsayin dabi’a ta daban, face a matsayin wata kadara dake tainaka wa wajen bunƙasa ayyukan raya kasa.
A dukkanin wuraren da yayi aiki, da yadda ya girmama jama’a, ba buninda a halin yanzu, labarin nagartarsa ya shuɗe a tsakanin al’umma, wanda ko shakka ba bu haka na nuninda cewar nagarta ita ke ɗauka alhakin riƙe wannan al’umma, kuma tana taka rawar gani wajen yanke hukunci, samar da daidaito da inganta mu’amala tsakanin cibiyoyi hatta a tsakanin ƙasashe.
A wajen DCG Isah Gusau kuwa, kyakyawan tsari yana taimakawa wajen yin zabi na gari koda kuwa a wuri mai wahalar sha’ani, wannan shine ya sabunta tsarin shugabanci daga karfin iko zuwa halasci. Hakazalika halasci shine ke sanya tsari ya gudana ko da ana tsaka da fuskantar ƙalubale.
Abu na farko daga cikin sauye-sauye mafi mahimmanci a lokacin mulkinsa shine sauyawa daga aikin tilasta bin doka zuwa ayyukan leƙen asiri. A al’ada, hukumomin tilasta bin doka sun dogara sosai kan bincike na yau da kullun da hanyoyin yau da kullum da suka fi ƙarfin fasahar hanyoyin sadarwa, wadanda da su ne ake gano laifuka na cikin gida da kuma ƙasashen waje.
Tsarin da DCG Isah Umar Gusau yazo da shi ya wargaza duk wani gurɓataccen shiri wanda ke kawo barazana ga tsaron ƙasa da kuma cigabanta. A bisa ga haka, sai ya ƙarfafa tsarin leƙen asiri, aiwatar da aiki cikin ƙwarewa da kuma gaskiya ya zama wajibi. A lokacinsa aka sa mu binƙasar fasahar gano jigilar kayayyaki masu haɗari kafin shigar su cikin ƙasa. Sa’annan aka samar da hanyar bin diddigin duk wani motsin jigilar kayayyaki a iyakoki da kuma garuruwa cikin sauƙi, haɗi da wargaza hanyoyin sadarwar ɓara garin da ke ƙoƙarin kawo wa ƙasa cikas kafin su yi aikin su.
Wannan canjin ya nuna nagartarsa da kuma jajircewa matuƙa, wajen bunkasa aiki ta hanyar amfani da falsafa. Domin haka, tabbas samar da tsaro ba ya nufin mayar da martani ga barazana sai dai yin shiri kafin faruwar fargaba.
Sanin kowa ne, cimma nasara game da kowanne tsarin aiki mai inganci yana buƙatar ma’aikata masu ƙwarewa. Yanayin kamun ludayin DCG Isah Umar Gusau ya mai da hankali kan tura mutanen da suka dace zuwa ga ayyukan da suka dace dasu, ta hanyar nuna fifikon ƙwarewa fiye da sanayya ko kuma alfarma. A cikin yanayi na matsalar tsaro, wannan salon bayar da ayyuka yana da matuƙar muhimmanci. DCG Gusau ya sani cewar kaucewa nagartaccen tsari a sha’anin tsaro, ba ƙaramar barazana bace ga tsaron ƙasa.
Daga nazarin leƙen asiri zuwa gano laifukan da suka shafi hada-hadar kuɗi, tabbatar da ingancin ma’aikatu ya dogara ne akan bunƙasa ƙwazon ma’aikata. Wanda wannan yana daga cikin ababen da DCG Isah Gusau ya mayar da hankalinsa akai—musamman ta fannin ƙarfafa iya aiki da kuma jaddada ci gaba da goya wa ƙwararru baya, domin tabbatar da cewa an tsara aiki da kyau da aiwatar da shi yadda ya kamata.
Safarar makamai, safarar miyagun ƙwayoyi, farautar namun daji da nufin cutar da su, da kwararar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba suna faruwa a yankuna, kuma suna haifar da giɓi mai muni. Da yake DCG Gusau ya fahimci haka, sai ya ƙirƙiro wani tsari na haɗin gwiwa tsakanin hukumomi na gida da kuma na ƙasashen duniya wanda aka gina bisa aminci da haɗin gwiwa.
Domin yin aiki tare da hukumomin cikin gida da abokan hulɗa na duniya, ya mayar da hankali kan raba bayanai, daidaita ayyuka, da ɗaukar mataki iri daya ko kuma na bai-daya ya taimaka wurin magance irin waɗannan matsaloli. A cikin wannan tsari, haɗin gwiwa ba ƙarin aiki bane, amma kuma yana da matuƙar muhimmanci.
Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da DCG Gusau ya samar ya ta’allaka ne da ƙarfafa tsarin yaƙi da satar kuɗi da kuma yin babakere akan kuɗaɗen yaƙi da ta’addanci a Najeriya, sai ficewar Najeriya daga jerin sunaye na FATF wanda ya nuna wani muhimmin ci gaba mai cike da tasiri ta hanyar bin ƙa’idojin doka. Domin kasancewa cikin jerin sunayen yana nuna raunin tsarin gudanar da ayyukan tsaro a ƙasa. Yana takaita kwararar kuɗi, yana hana masu zuba jari, kuma yana rage amincewar duniya.
Duk da haka, fita daga jerin sunayen yana nuna wani abu mafi ƙarfi: cewa tsarin yana aiki.
Ta hanyar ƙoƙarin haɗin gwiwar cibiyoyi—wanda ya ƙunshi sassan leƙen asiri na kuɗi, jami’an tsaro, da hukumomin da ke kula da harkokin kuɗi—Najeriya ta nuna ikonta na cika ƙa’idodin duniya. Darasin a bayyane yake, an gina shi ta hanyar tsarin da aka daidaita, aka aiwatar, kuma aka ci gaba da dorarwa.
A duniyar da ke da alaƙa da juna a yau, tsarin analogues wato tsarin da ba bu fasaha a ciki basu isa a yi amfani dasu ba yanzu ba. Fahimtar da DCG Gusau ya yiwa fasahar zamani da kuma irin rawar da take takawa a harkokin tsaron kan iyakoki na zamani, yasa shi mayar da hankalinsa kacokam wajen tabbatar an yi nasara a fannin.
Tun daga sarrafa tsarin bayyana kuɗi ta kai tsaye zuwa tura fasahar bibiya ba tare da bude kofar kutse ba, ta yi amfani matuƙa—musamman ta hanyar yin amfani da kayan aikin na zamani don haɓaka inganci, daidaito, da tattara bayanai a kankanin lokaci. Fasahar, a wannan mahallin, ba wai kawai mai ba da gudummawa ba ce – ababen more rayuwa ce.
Tana ba cibiyoyi damar gudanar da ayyukan su ta hanyar kwarewa. Tana ba da damar gani, gano abubuwa, da kuma ikon gano alamu waɗanda in ba haka ba za su kasance a ɓoye. A ƙarƙashin jagorancin shugaban Kwastam na yanzu, Bashir Adewale Adeniyi, wannan sauyin fasahar zamanin yana ci gaba da ingantuwa yana ƙarfafa hanyar zuwa ga cikakken tsarin gudanar da hukumar kwastam.
A ƙarshe, ana auna shugabanci na gaskiya ta hanyar abin da ke dorewa bayan wa’adin shugabancin mutum ya ƙare.
A nan ne falsafar DCG Gusau ta fi samun bayyanuwa a tsakanin al’umma. Ta hanyar haɗa tsare-tsare – maimakon dogaro da ikon mutum ɗaya—wanda hanyar da ya bi har yanzu tana tabbatar da ci gaba. Yana ba da damar ci gaba ba tare da rasa alkibla ba. Ya kawo gyare-gyare daga shirye-shiryen wucin gadi zuwa na dindindin. Hakanan yana sake fasalin rawar da jagoranci ke takawa.
Tsaron Ƙasa: Yadda DCG IG Umar Yayi Amfani Da Falsafa Wajen Jagorantar Ingantaccen Sauyi A Kwatsam
Date: