Mun aike da sakamakon ‘yan Majalisar dokoki ta kasa cikin nasara, amma na shugaban kasa yaki yiwuwa.
Wani ma’aikacin wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ya shaidawa kotun dake sauraran shari’ar zaben shugaban kasa cewa, sunyi kokarin tura sakamakon zaben shugaban kasa ta hanyar amfani da na’urar BVAS amma yaki tafiya.
Shaidar wanda yabayyana gaban kotun bisa bukatar Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar, ya Kara da cewa yayi nasarar tura sakamakon zaben ‘yan Majalisar Dattawa dana wakilai batareda tangarda ba, duk kuwa da cewa rana guda akayi zaben dana Shugaban kasa.
Acewarsa, bayan warewa tareda kirga kuri’un, ya shigar da bayanansu cikin fom din EC8A Wanda wakilan jam’iyyu da jami’an tsaro suka sanyawa hannu, inda daga baya yadauki hotunansu sai dai na’urar ta BVAS ta gaza aikewa da bayanan wanda hakan tasanya yamika sakamakon a takarda ga mai tattara sakamakon zaben na mazaba.
Jaridar DAILYFEEDS ta rawaito cewa, Dayake amsa tambaya daga lauyan hukumar INEC, shaidan yabayyana cewa an koya masa yadda zai tura sakamakon koda babu network wanda yahada da saka hoton takardar sakamakon, yakara da cewa da zarar an samu network sakamakon zai tafi Kai tsaye.
Da lauyoyin Bola Tinubu da APC ke masa tambayoyi akan yadda zaben yakasance a yankinsa, sai yace bai samu matsala ba kasancewar akwai jami’an ‘yansanda dake gadinsa a lokacin.