Kungiyar tsaro ta NATO na gudanar da wani atisayen jiragen saman yaki.
Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta fara gudanar da wani atisayen jiragen saman yaki a sararin samaniyar Turai.
Atisayen wanda Jamus take jagoranta, ya kunshi jiragen saman yaki 250 daga kasashe mambobin kungiyar 25.
Akalla matuka jiragen saman yaki da masu taimaka musu 10,000 ne zasu shiga wannan atisaye.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ake cigaba da yiwa juna kallon hadarin Kaji tsakanin kasashen yammacin duniya da Rasha tun bayan kutsen da Rashan tayiwa kasar Ukraine shekarar data gabata.