Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaTajudden Abbas yazama kakakin majalisar wakilai ta goma

Tajudden Abbas yazama kakakin majalisar wakilai ta goma

Date:

Tajudden Abbas yazama kakakin majalisar wakilai ta goma

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Zaria Hon Tajudden Abbas ya lashe zaben da akayi na shugabancin majalisa ta goma wanda ya gudana lokacin kaddamar da majalisar wakilan a talatar nan.

Dan majalisa Abbas na Jam’iyyar APC wanda kuma shine dantakarar fadar shugaban kasa, ya lashe zaben ne da kuri’u 353 inda yakayar da tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilan data gabata Ahmed Idris wase wanda yasamu kuri’u 3.

Wanda yazo na uku Aminu Jaji Shima ya samu kuri’u 3 daga cikin kuri’u 359 da aka kada.

Tunda fari dai Mukhtar Betar, da Yusuf Gagdi, da Miriam Onuoha da kuma Sada Soli wadanda suka tsaya takarar sun janyewa Tajudden Abbas.

Kodayake an kai ruwa rana da Betara kafin daga bisani yamika wuya ya amince da janyewar.

Tsohon shugaban masu rinjaye kuma dan majalisa mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa Hon Alhassan Ado Doguwa, shine wanda yafara hakura da burinsa na shugabantar majalisar ta goma.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories