Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Sani Dambo shugaban hukumar haraji.
Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alh Sani Abdulkadir Dambo amatsayin sabon shugaban hukumar tattara kudaden haraji ta jihar (KIRS).
Dambo wanda yataba rike wannan mukami a tsohuwar Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje, kwararre ne a fannin tattara haraji inda yake rike da mukamin babban manaja mai lura da binciken haraji a hukumar haraji ta kasa (FIRS) Abuja.
Dambo ya kammala digirinsa afannin Akanta da sarrafa kudade, ya kumayi digirinsa na biyu a fannin kasuwanci.
Cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, Sabon shugaban hukumar ta tattara kudaden shigan ta kano, mamba ne a cibiyar bincike kan haraji ta kasa, kuma yanada kwarewar aiki ta tsawon shekaru 20.
Agefe guda, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya nada Alh Isiyaku Kubarachi amatsayin sabon shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA).
Dukkanin mukaman biyu dai sun fara aikine nan take.