Thursday, April 30, 2026
HomeDa dumi dumiShugaba Tinubu zaije kasar Faransa domin halartar taron tattalin arzikin duniya... ...

Shugaba Tinubu zaije kasar Faransa domin halartar taron tattalin arzikin duniya… Fadar shugaban kasa

Date:

Shugaba Tinubu zaije kasar Faransa domin halartar taron tattalin arzikin duniya.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Najeriya a ranar alhamis zuwa Faransa domin halartar wani taron musamman kan sabuwar yarjejeniyar hada hadar kudade ta duniya.

Taron na kwanaki biyu, zai maida hankali ne kan yadda za’a fitar da sabbin dabaru musamman ga kasashen dake fuskantar matsalolin kasafin kudi na gajeren zango.

Mashawarci na musamman ga shugaban kasar kan harkokin sadarwa shine yabayyana batun balaguron shugaban kasar a wani jawabi daya fitar a ranar litinin.

Wannan ne dai karon farko da shugaban zai bar Najeriya a hukumance domin halartar wani taro a kasashen waje.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories