Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maida Barr Muhyi kan mukaminsa na shugabancin hukumar yaki da rashawa.
Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya amince da mayarda Barista Muhyi Magaji Rimin Gado kan mukaminsa na shugabancin hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano PCACC domin karasa wa’adi na biyu na shugabancin hukumar.
Wannan yazo ne cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Idan za’a tuna dai tsohon Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shine yadakatar da Muhyi Rimin Gado bisa zargin aikata ba dai daiba, abinda yasanya Muhyin garzayawa zuwa kotu domin neman ta soke wancen hukuncin da gwamnatin ta dauka.
A watan Mayun daya gabata ne dai kotu ta yanke hukuncin maida Barista Muhyi kan kujerarsa ta shugabancin hukumar ta PCACC.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maida Barr Muhyi kan mukaminsa na shugabancin hukumar yaki da rashawa.
Date: