Jam’iyyar APC tayi kira ga tsohon Gwamna Ganduje dayayi watsi da gayyatar da Muhyi yayi masa
Jam’iyyar APC a Jihar Kano, tayi kira ga tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje dayayi watsi da gayyatar da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa PCACC tayi masa.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa mai dauke dasa hannun shugaban Jam’iyyar Abdullahi Abbas da sakataren Jam’iyyar Zakari Sarina.
Jam’iyyar tace sake dawo da batun bidiyon Dala awannan lokaci da maganar ke gaban kotu, ba komai bane face kokarin batawa tsohon Gwamnan suna.
Jam’iyyar ta kara da cewa, anyi makamancin hakan a zaben shekarar 2019 domin hana Ganduje tsayawa takara.
Awannan karo acewar APC, Jam’iyyar NNPP na wannan yunkuri ne domin shiga tsakanin tsohon Gwamnan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda gudane cikin ‘yan gaba gaba a tallatashi daga Arewacin Najeriya.
Jam’iyyar ta cigaba da cewa, akwai kyakkyawar alaka tsakanin Ganduje da Bola Tinubu tun daga lokacin daya fito takara har kawo yanzu.
Wannan dai na zaman martani ga gayyatar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kano ta aikewa tsohon Gwamnan domin yabayyana gabanta tareda kare kansa kan fefan bidiyon da ake zargin yana karbar kudaden kasashen waje.
Jam’iyyar APC tayi kira ga tsohon Gwamna Ganduje dayayi watsi da gayyatar da Muhyi yayi masa
Date: