Friday, June 26, 2026
HomeSiyasaKungiyoyin gwagwarmaya na goyon bayan gayyatar da akayiwa Ganduje kan bidiyon Dala

Kungiyoyin gwagwarmaya na goyon bayan gayyatar da akayiwa Ganduje kan bidiyon Dala

Date:

Kungiyoyin gwagwarmaya na goyon bayan gayyatar da akayiwa Ganduje kan bidiyon Dala

Kungiyoyin dake gwagwarmayar kare hakkin Dan Adam sun nuna goyon bayan sake dawo da bincikar tsohon Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da ake zargi ya karbi cin hanci ta cikin wani fefan bidiyo daya bulla a shekarar 2018.

Comrade Kabir Dakata na cibiyar samar da daidaito da adalci CAJA, na cikin masu goyon bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kano PCACC akan cigaba da binciken tsohon Gwamnan.

Comrade Dakata wanda yabayyana hakan ta cikin Shirin Akwana atashi na tashar talabijin ta Tambarin Hausa, yace gudanar da bincike zai zama adalci ga shi kansa tsohon gwamna Ganduje, da gwamnati dama al’ummar jihar Kano.

Comrade Kabir Dakata yacigaba da cewa ” a shekarar 2021 na taba yiwa Ganduje wannan tambayar akan ya amince acigaba da binciken domin wanke kansa daga zargi, amma yaki amincewa”.

“Abin bakin ciki ne ace jihohin kudancin Najeriya na saka fefan bidiyon a shatale tale suna nuna tsohon Gwamnan” inji Comrade Dakata.

A ranar alhamis ne dai Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano PCACC, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace sun aike da takardar gayyatar tsohon Gwamna Ganduje domin ya amsa wasu tambayoyi, lamarin daya janyo zafafan martani daga wasu bangarori ciki harda Jam’iyyar APC wadda tace kada tsohon Gwamnan ya amsa waccen gayyata.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories