Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago yace hukumar sa zata yi amfani da sashin dokar ma’aikatar wajen tursasawa tare da magance dabi’ar zubar da shara da tsakar dare a wuraren da basu kamata ba a jihar.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai lokacinda ma’aikatan hukumar ke tsaka da aikin kwashe sharar dake fagge ‘yan Alluna.
Cikin Wani jawabi da aka rabawa manema labarai mai dauke dasa hannun Jami’in yada labaran hukumar Kamal Umar Kurna,Ambasada Dan zago yace abin takaici ne yadda wasu surika bin dare suna jibge sharar akan titunan birnin Kano da wuraren da basu dace ba musamman wuraren da aka kwashe sharar tun da farko.
A bayanansu tunda farko mazauna kasuwar ta fagge ‘yan Alluna sun yaba da yadda aikin kwashe sharar yake gudana a fadin jihar nan Koda dai wasu daga cikin su sun bayyana cewa kamata gwamnati ta gudanar da aikin tuntuni.
Daga cikin wuraren da hukumar kwashe sharar tayi aiki a yau sun hada da fagge ‘yan Alluna, karkashin gadar kasuwar Bata da New Road dake Unguwar Sabon Gari.