Thursday, April 30, 2026
HomeMuhalliGwamnatin Kano tasha alwashin kawo karshen duk wata shara dake gefen tituna

Gwamnatin Kano tasha alwashin kawo karshen duk wata shara dake gefen tituna

Date:

Gwamnatin jihar Kano tasha alwashin kawo karshen duk wata shara dake gefen tituna

Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago yace, nan da mako guda al’ummar jihar nan zasu shaida yadda hukumar sa zata kwashe dukkanin wata shara dake jibge akan titunan jihar nan domin gujewa ambaliayr ruwa.

Dan zago ya bayyana hakan lokacin da tawagar ‘yan jaridun dake aiki a gidan gwamnatin jihar Kano suka Kai masa ziyarar aiki a ofishinsa.

Yace duba da irin ayyukan da hukumar sa ta gudanar tun bayan daya karbi ragamar ta, al’ummar jihar Kano nada kyakkyawan zato da Sanya rai akan aikace aikacen a yanzu wanda hukumar tasa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen share musu hawayensu.

Da yake nasa jawabin tun da farko shugaban ‘yan jaridun dake gudanar da ayyukansu a gwamnatin kano Adamu dabo dawakin tofa yace sun kawo ziyara a mataki na ba zata domin ganewa idanunsu irin aikace aikacen hukumar.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories