Gwamwamnatin jihar Kano ta Sha alwashin kwashe dukkanin shara tare da tsaftace gidan ajiye namun daji na Kano wato gidan Zoo.
Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago ne ya bayyana hakan lokacin da shugaban hukumar gudanarwar gidan ajiye namun dajin na Kano Sadik Kura Muhammed ya kai masa ziyara domin neman taimakon hukumar kwashe sharar.
Acikin wani jawabi mai dauke dasa hannun Jami’in yada labaran hukumar Kamal Umar Kurna, ya rawaito Ambasada Dan zago na cewa, alhakin hukumar sa ne kwashe shara a fadin birnin Kano matukar an tuntubi hukumar tasa ta hanyar data dace, a dan haka duba da yadda gidan ajiye namun dajin yake da alfanu ta hanyoyi da dama ga al’ummar Kano hukumar sa zata yi abinda ya dace cikin kankanin lokaci.
Da yake nasa jawabin tun da farko shugaban hukumar gudanarwar gidan ajiye namun dajin Sadik Kura Muhammed yace ya je hukumar ta REMASAB ne domin neman daukin ta, kasancewar dabbobi da al’ummar dake ziyarar gidan na namun dajin suna fuskantar matukar kalubale saboda yadda shara take neman shafe gidan.
Gidan ajiyar namun dajin dai na zaman wata cibiya ta shakatawa da yawon bude idanu ga al’ummar Kano dama bakin dake shigowa daga makwaftan jihohi.