Kwamandan rundunar ‘yansandan kasar nan ta Mopol 9 dake hotoro Jidda Sanusi ya bayyana gamsuwa da yadda ayyukan hukumar kwashe shara ta jihar Kano yake gudana a fadin jihar nan.
Sanusi ya furta hakan ne lokacin da ma’aikatan hukumar kwashe sharar suke gudanar da ayyukansu a cikin barikin ‘yansandan dake hotoro.
Jidda Sanusi yace sharar ta kwashe fiye da shekara 1 da Rabiba tare da hukumomin da abin ya shafa sun waiwaye ta domin kwashewa ba, amma kasa da awanni 24 da jagorancin barikin nasu ya Mika kokensa ga shugabancin hukumar na yanzu anzo an kwashe musu sharar.
Da yake jawabi tun da farko shugaban hukumar kwashe sharar ta da tsaftar muhalli ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago yace hakkin hukumar sa ne ta kawar da shara a kowane lungu da Sako dake jihar nan ciki kuwa har da barikokin jami’an tsaron dake jihar nan matukar anbi hanyar data dace wajen sanar da hukumar sa.