Kasuwar Magani a Kano Anyi Canjin Rigar Mahaukaci
Wato mahaukaci ne yana tafiya da rigarsa mai dama-dama sai ya hango Wata rigar mai ƙazanta akan Bola (Juji) abinka da mai lalura Sai ya kwaɓe tasa mai dama-dama ya sanya Mai ƙazanta.
Wato Masu harkar magani a birnin Kano sunada ƙorafe-ƙorafe akan shirin gwamnatin tarayya wajen canzawa masu saida magani da kuma kasuwancin magani matsuguni zuwa Kasuwar Ɗangwauro.
Babban ƙorafin yan kasuwar na farko shine rashin tanadar wa yankasuwa masu ƙaramin ƙarfi matsuguni na biyu Farashin shago a kasuwar na uku nisa. Wannan shine babban ƙorafin yan kasuwa.
Duk mai neman kawo gyara a wannan lamari abin da zaiyi na farko shine samarda rukunin kananan yan kasuwa wato gyara kuskuren da akayi a Ɗan Gwauron,ba gina wata sabuwa ba.
Naga Allo da gwamnatin jiha ta kafa a cikin sabon Gari kan titin New road na yumƙurin Gina sabuwar kasuwar Magani a tsohuwar tashar manyan motocin Inyamurai. Wannan yunƙuri komawa Baya ne saboda wurin yayi ƙanƙanta sosai kuma Makarantu ne a kewaye da filin babu sararin faɗaɗa kasuwar saidai ta sama.
Wani muhimmin Al,amari kuma shine farashin shago wanda na samu labarin yakai Naira miliyan talatin da biyar wannan shine ba,a rabu da bukar ba an haifi habu.
Kuma a wannan filin tashar za,a gina Camp na Ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Kano pillars. Ɗakunan kwana da ƙaramin filin atisaye kenan a fahimta ta,kamar yadda Allon da aka kafa ya nuna. A Gaskiya wannan wuri ya matse Sosai.
Duba da wadannan dalilan muna kira ga gwamnatin jiha data dubi lamarin da idon basira domin kyautata wancan kasuwar ta Ɗan Gwauron yadda za,a shigo da tanadin ƙananan yan kasuwa ɓangaren samun shaguna masu sauƙin farashi. Kar nan Gaba kaɗan azo ana tashin Makarantu domin faɗaɗa kasuwar Magani.
Daga karshe wannan tsohuwar tashar dai an tasheta ne saboda dalilai na tsaro da kuma ragewa birni cinkoso. Kabilar da aka tasa Daga wajen dama suna ganin harkar magani tasu ce hausawa kutse suka musu,me kake gani kuma zai faru an maida kasuwar cikinsu? Mudai yan Kasuwa Saniya ce da bata da Jela Allah shike kore mata Ƙuda.
Ibrahim Usman Ilelah
ibb6375@gmail.com