Bazamu lamunci sakaci da aiki Atsakanin Malamai da Shugabannin Makaranta ba..
Gwamnatin Jihar Kano tace bazata lamunci sakaci da aiki a tsakanin Malamai da Shugabannin Makarantun dake Jihar ba.
Kwamishinan Ma’aikatar ilimi na Jihar Hon Umar Haruna Doguwa shine yayi wannan gargadi lokacin wani taron masu ruwa da tsaki kan makomar ilimin mata wanda yagudana a rufaffen dakin taro na Sani Abacha dake Kofar Mata.
Doguwa yace, daga yanzu babu wani dalili da zaisa ‘Yan Makaranta su makara, kasancewar Gwamnati ta tanadi manyan motocin bas da zasu dinga jigilar daliban akoawace rana, inda yaja hankalin iyaye akan sanya idanu kan karatun ‘ya’yansu akoda yaushe.
Anata bangaren, Haj Ladidi Fagge Sakatariyar Kungiyar HILWA data kunshi fitattun mata ‘Yan asalin Jihar Kano, ta kalubalanci iyaye mata akan halin da ‘yammata ke ciki ayanzu, inda ta alakanta rashin zuwan yara mata da yawa makaranta da kwadayin abin duniya.
Taron na hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar ilimi da takwararta Ma’aikatar Mata, ya samu halartar kungiyoyi da daidaikun mutane a fannin na ilimi da zamantakewa.