Friday, June 26, 2026
HomeWasanniShugaban Kwamitin Wasanni Na Majalisar Wakilai ya Bukaci Super Eagles da Su...

Shugaban Kwamitin Wasanni Na Majalisar Wakilai ya Bukaci Super Eagles da Su Samu Cikakken Maki a Wasansu da Libiya

Date:

…Yayin da Hon. Maipalace Ya Nuna Karfin Gwiwa da Super Eagles Kafin Wasannin Neman Cancantar Shiga Gasar Kofin Afrika

Sabon Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Wasanni, Honourable Kabiru Amadu, ya yi kira ga Super Eagles da su yi nufin samun maki shida a wasannin neman cancantar shiga gasae nahiyar Afirka (AFCON) na tsallakewa da za su buga da Libiya.

Super Eagles za su kara da kungiyar Mediterranean Knights ta Libiya a wasan neman cancanta na nahiyar na uku da za a yi a ranar Juma’a a filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo. Za a sake buga karawar a ranar Talata mai zuwa a Benghazi, Libiya.

Da yake magana kan wasannin da ke tafe, Honourable Amadu, wanda ke wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta Jihar Zamfara, ya nuna gamsuwarsa da kwarewar tawagar Najeriya wajen samun nasara a wasannin biyu.

Ya bayyana cewa Super Eagles suna da duk abubuwan da ake bukata don cimma burin nasara, kuma ya bukaci su nuna basirarsu a fili.

“Babu shakka zan yi alfahari da ‘yan wasanmu a wasan da za su yi da Libiya, musamman idan aka duba rawar da suka taka a wasannin da suka gabata,” in ji dan majalisar. “Na yi matukar farin ciki da abin da na gani a wasan da suka buga da Jamhuriyar Benin a Uyo, sannan kokarin da suka yi a wasan da suka buga da Rwanda a Kigali ya burge ni, duk da sakamakon kunnen doki.”

Ya kara da karfafa tawagar da su gina kan nasarorin da suka samu a baya, tare da yin koyi da wannan a wasannin da ke tafe.

“Na yi tsammanin za su inganta kokarinsu a wannan Juma’ar, su ci gaba daga inda suka tsaya a wasannin da suka gabata. Har ila yau, ina so ‘yan wasan su sani cewa, a matsayinmu na ‘yan majalisa, Majalisar Wakilai tana cikakken goyon bayan su, kuma Shugaban Majalisar, Honourable Tajudeen Abbas, na tare da su don su faranta wa ‘yan Najeriya rai.”

Najeriya tana kan gaba a rukunin D na jadawalin cancantar shiga gasar zakarun nahiyar Afirka da maki hudu daga wasanni biyu, kafin karawarsu mai mahimmanci da Libiya ranar Juma’a.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories