Gwamnatin Jihar kano ta Shiryawa Jami’an Yada Labarai Bita akan Cimaka
Awani bangare na kara inganta ayyukan jami’an yada labarai na kananan hukumomi, ma’aikatar yada labarai da al’amuran cikin gida ta jihar kano ta shirya Bita ta kwanaki biyu ga jami’an akan cutukan da akan gamu dasu sakamakon rashin cin abinci mai gina jiki.
Dayake gabatar da makala yayin bitar, Dr Abubakar Hamza Ahmad na ma’aikatar lafiya ta jihar kano yayi bayani akan cutukan da suka addabi al’umma da suka hadarda hawan jini, ciwon shuga, sikila da sauransu wadanda cutuka ne da wani baya yadawa wani sai dai ko gado ko Kuma rashin kulawa da lafiya.
Yace”Akwai cutuka wadanda wani bazai sakawa wani ba kamar kansa, sikila, shuga, hawan jini da sauransu. “
“Akwai sama da mutum miliyan 11 dake dauke da cutuka irin wadannan a fadin duniya wanda kusan kaso 30 cikin dari suka fito daga Nageriya.”
A nasa jawabin, kwamishinan yada labarai Comrade Ibrahim Abdullahi Wayya yace, wannan bita hadin gwiwa ce tsakanin ma’aikatarsa da ma’aikatar lafiya da wasu kungiyoyin masu zaman kansu.
Yace hikimar itace a wayar wa da jami’an yada labaran hanyoyin da zasu bi wajen aikewa da sako a fannin kulawa da inganta abinci a kananan hukumomin da suka fito.
Jaridar Dailyfeeds Hausa ta rawaito cewa, jami’an yada labarai daga dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar kano suka halarci taron bitar.