2027: Kungiyar Tsoffin Shugabannin Kananan Hukumomin Kano ta Musanta Goyon Bayan Sanata Barau
Kungiyar Tsofaffin Shugabannin Kananan Hukumomi na Jihar Kano (ALGON Integrity Group) ta karyata wani rahoto da ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa tsoffin shugabannin sun amince da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a 2027.
A wata hira da manema labarai, Shugaban Kungiyar kuma tsohon shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Hon. Hassan Garban Kauye Farawa, ya bayyana rahoton a matsayin maras tushe.
Ya Kuma yi kira ga mambobin APC a Kano da fadin Najeriya da su yi watsi da rahoton daya kira marar inganci.
Hon. Hassan Garban Kauye Farawa ya bayyana cewa a daidai lokacin da ake ikirarin an gudanar da taron nuna goyon bayan a Abuja, mafi yawan tsoffin shugabannin kananan hukumomi suna nan a Kano, suna halartar tarukansu na yau da kullum.
“Abin mamaki ne, kuma gaskiya abin dariya ne, ace an yi taro a Abuja alhalin muna nan Kano ana ganin mu a fili,” in ji shi.
Ya jaddada cewa jam’iyyar APC na da tsari da tsarin shugabanci mai karfi, wanda tsohon Gwamnan Kano, tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, kuma jagoran siyasar jam’iyyar a Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, tare da sauran manyan jiga-jigai, ke jagoranta.
Ya nanata cewa shugabancin jam’iyyar da aka amince da shi kadai ke da ikon bayyana hanyoyi da sharuddan da za a bi wajen zaben ‘yan takara.
Hon. Hassan Garban Kauye ya yi Allah-wadai da yunkurin wasu daidai kun mutane ko kungiyoyi da ke son tayar da hankali ko rikice-rikice a cikin jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan wani yunkuri ne na kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yan Jam’iyyar APC.
Ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da jajircewa, hadin kai, tare da mayar da hankali wajen karfafa jam’iyyar APC yayin da ake cigaba da shirye-shiryen tunkarar kakar zaben 2027.
Idan za’a iya tunawa kwanakin baya tsoffin ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano da kuma tsoffin kwamishinonin da suka yi aiki a karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje sun fitar da makamanciyar wannan sanarwar, inda su ma suka musanta batun marawa Sanata Barau baya a takarar gwamna ta 2027.