Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaDan Majalisa Ya Raba Buhunan Shinkafa 10,000 a Rano, Kibiya da Bunkure

Dan Majalisa Ya Raba Buhunan Shinkafa 10,000 a Rano, Kibiya da Bunkure

Date:

Dan Majalisa Ya Raba Buhunan Shinkafa 10,000 a Rano, Kibiya da Bunkure


Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Kabiru Alhassan Rurum( Turakin Rano), ya raba buhunan shinkafa ga mutane fiye da dubu goma a yankunan da yake wakilta domin tallafa musu a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan.

Rahotanni sun ce an gudanar da rabon tallafin ne a sassa daban-daban na kananan hukumomin uku, inda dubban al’umma suka amfana da shirin.

A cewar dan majalisar, matakin ya biyo bayan halin matsin tattalin arziki da ake ciki da kuma karuwar bukatun abinci a lokacin azumi.

Ya bayyana cewa tallafin na da nufin rage radadi da saukaka wa al’ummar yankinsa a wannan lokaci mai muhimmanci.

Sanarwar da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Fatihu Yusuf Bichi, ya fitar ta ce Turakin na Rano ya kuma bukaci sauran masu hannu da shuni da masu rike da mukaman gwamnati da su taimaka wa al’umma, musamman a watan Ramadan, domin hakan abu ne mai falala.

Baya ga rabon kayan abinci a farkon azumi kowacce shekara, dan majalisar kan raba atamfofi da shaddoji ga al’umma a lokacin bukukuwan Sallah domin kara faranta zukatan jama’a a Rano, Kibiya da Bunkure.

Al’ummar yankunan sun nuna jin dadinsu tare da godewa dan majalisar bisa tallafin da yake aikewa gida-gida domin tallafa musu

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories