Wani ma kusancin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, Alhaji Bashir Abubakar ya mayarwa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje martani bisa maganar da ya faɗa cewar bai san jam’iyyar da zai miƙawa mulkin jihar Kano ba, a ranar 29 ga watan Mayu.
Alhaji Bashir wanda ɗan’uwa ne ga zaɓaɓɓen gwamnan, ya ce bayanin da Gwamna Ganduje yayi kaɗai ya isa ya tabbatar masa da kuma al’ummar jihar Kano cewar haƙika gwamna shi kuwa ya san wa zai bawa mulkin jihar a ranar da zai sauka daga kan mulki a matsayin gwamna.
Ya ƙara da cewa, ambaton jam’iyyar NNPP da yayi kaɗai da farko kafin ya ambaci jam’iyyar sa ta APC shine ɗaya daga cikin manyan amsoshin da gwamnan ya kamata ace yayi la’akari dasu cewar NNPP itace halattacciyar jam’iyyar da zai miƙawa mulki a wata mai kamawa.
Alhaji Bashir ya ƙara da cewa, Gwamna Ganduje da sauran waɗansu mutane na jam’iyyar APC a Kano maganganun da suke yi dangane da nasarar da Allah Ya baiwa Abba Kabir Yusuf ako da yaushe, suna alamtawa al’umar Kano da Najeriya cewa imanin da suke nunawa abaya cewa za su yi, da hukuncin da Ubangiji ya zartar dangane duk wanda Allah Ya zaɓa, ba gaskiya bane, kuma ba, kuma hakan ya nuna ba suyi imani da ƙaddara ba.
Yace abin mamaki ne da Gwamna Ganduje bayan dan takarar jam’iyyar APC da kansa Nasiru Yusuf Gawuna ya fito ya taya zaɓaɓɓen gwamna murna ya kuma yi masa fatan alkhairi daga baya Gandujen ya fara kokarin tayar da zaune tsaye a Kano, wanda a shekarun sa da kuma gogewar da yake cewa yana da ita a siyasa da kuma aiki, ba daidai ne a riƙa ganinsa yana irin haka ba.
Alhaji Bashir yace irin maganganun da Gwamna Ganduje yake yi za su iya harzuƙa magoya bayan jam’iyyar APC tare da ɗora su akan wani gwadabe na kin yarda da hukunci na ubangiji da kuma hukumar zabe mai zaman kanta wanda itace ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan jihar Kano ka iya jefa Kani cikin haɗari.
Har ma ya bayar da shawara cewa Yakamata hukumomi su ringa sanya idanu a da kuma bibiyar irin kalaman gwamna Abdullahi Umar Ganduje tare da yin kokari wajen tsawatar masa ko kuma ɗaukar mataki akan sa, a inda ya kamata.
Alhaji Bashir Abubakar ya kuma zargi Abdullahi Umar Ganduje da yiwa jam’iyyar sa ta APC da mataimakin sa Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya fito neman kujerar Gwamnan Kano maƙarkashiya – yana mai cewa tsawon lokacin da akayi ana yaƙin neman zaɓe ba’a ga Gwamnan ba a wuraren da akayi yaƙin neman zaɓe tare da Gawuna ba, sai daga baya lokacin da dan takarar ya janye ne Gwaman Ganduje ya fito yana mai kokarin zuga mataimakin nasa da cewar kada ya amince da hukuncin da kuma sanarwar da hukumar zabe mai zaman kanta tayi, wanda hakan kokari da gwamna Ganduje yake yi na dakushe da kuma lalata tasirin siyasar Nasiru Yusuf Gawuna a jihar Kano, amma da alama Gawuna bai fahimta ba.
Alhaji Bashir Abubakar ya tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf haƙiƙa shine wanda gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai miƙawa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Haka zalika makusancin na zaɓaɓɓen Gwamnan, Alhaji Bashir Abubakar, ya tunatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje cewar a kwanan baya ne, ya fito ya nemi tafiyar al’ummar jihar Kano akan kurakuran da yayi masu, wanda a cewar sa furta kalamai na tunziri irin wadannan za su iya dawo da irin tsana da kuma karfin ganin laifi da kuma baiken sa da al’ummar jihar Kano sukeyi wanda hakan zai iya janyo masa suyi rabuwa irin ta dutse a hannun riga.
Inda ya ƙara da cewa zai fi yiwa Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano mai barin gado, kyau idan yayi ƙoƙarin gamawa da al’ummar jihar Kano lafiya.
Ya kuma ce zai fi yiwuwa Abdullahi Umar Ganduje gwamnan jihar Kano mai barin gado kyau idan har ya dakata da furta irin wadannan kalamai na tunziri wadanda ka iya jefa jihar Kano a cikin wani hali da Allah ne kaɗai Ya san irin abinda zai iya faruwa sakamakon tunzura magoya bayan jam’iyyar APC da yake yi, da kuma ƙoƙarin haddasa faɗa tsakanin magoya bayan jam’iyyun guda biyu.
Ya ce idan har cigaban jihar Kano shine a gaban gwamna Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado wajibi ne ya dakata da irin wadannan halaye yabi tsari da kuma ra’ayi na mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna wanda a farko ya fito ya nuna yayi imani da ƙaddara saɓanin yanzu daya zuga shi kuma yake kokarin zuga dukkanin mutanen da suke goyon bayan jam’iyyar APC.
Ya kuma shawarce da cewar babban abinda ya kamata ƴan jam’iyyar APC na jihar Kano daga manyan su har ƙananan su suyi shine yin imani da ƙaddara tare kuma da kudurta cewa idan Allah ya kaimu wani zangon na zabe zasu fito su gwada sa’ar su.