An Zabi Nura Bala Ajingi Shugaban Wakilan Kafafan Yada labaran Majalisar Kano…
Kungiyar Wakilan kafafan yada labarai dake aiki a Majalisar Dokokin jahar kano ta Zabi Comrade Nura Bala Ajingi Wakilin Gidan Radio Kano a matsayin Shugaban kungiyar.
Da yake bayyana sakamakon zaben, Sakataren kwamitin zaben Abbas Musa Sheka daga Express Radio ya ce mafi yawan Wakilan sun kuma zabi Comrade Abubakar Shehu Kwaru daga gidan Talabijin na ARTV a matsayin sakatare sai kuma Musbahu Ahmad ma’aikacin Majalisa a bangaren daukar Hoto a matsayin Ma’ajin kungiyar.
A nasa jawabi jim kadan da zabar shugabannin, Sakataren Yada Labaran Majalisar Comrade Kamaluddeen Sani Shawai ya ja hankalinsu akan jajircewa tare da sadaukar da kai da kuma kare martbar Majalisar sannan ya yi alkawarin yin aiki tare da shugabanin domin samun kyakkyawan sakamako.
Ya kuma bukaci dukkanin ‘yan kungiyar su baiwa sababbin shugabanin cikakken hadin kai da goyon baya domin samun jagoranci nagari.
Da yake Jawabi a madadin wadanda aka zaba Shugaban kungiyar Comrade Nura Bala Ajingi ya nemi hadin kai da shawarari tare da yin aiki tare da ‘yan kungiyar domin cigaban aikin jarida.