Saturday, October 24, 2026
HomeDa Ɗumi-ƊumiGwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Habu Fagge shugaban hukumar fansho ta...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Habu Fagge shugaban hukumar fansho ta jihar

Date:

Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alh Habu Fagge amatsayin Sabon shugaban hukumar fansho ta jihar.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai mai dauke dasa hannun Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, yace nadin yafara aiki nan take.

Alh Habu Fagge tsohon shugaban hukumar tattara haraji ta jihar Kano, ya kammala digirinsa a fannin hada hadar kudi a jami’ar Abraham Lincoln dake Amurka.

Ya rike mukamai da dama a aikin gwamnati da suka hadarda daraktan kudi, da daraktan tsare tsare.

Alh Habu Fagge dai zai karbi ragamar hukumar ta Fansho ne adai dai lokacin da tsoffin Ma’aikata da sukayi ritaya ke kokawa akan rashin biyansu hakkokinsu da tsohuwar Gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi, zargin da gwamnatin tasha musawa.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories