Sunday, October 25, 2026
HomeJimamiGwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna alhinin rashin limamin waje shekh Nasir...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna alhinin rashin limamin waje shekh Nasir Muhammad Nasir.

Date:

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna alhinin rashin limamin waje shekh Nasir Muhammad Nasir.

Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da al’ummar Kano bisa rasuwar babban limamin waje shekh Nasir Muhammad Nasir.

Cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayin amatsayin malamin addinin islama dayasha bam bam da saura ta la’akari da irin Gudunmawar daya bayar wajen bunkasa addinin musulunci bama a Jihar Kano ko Najeriya ba, harma a fadin duniya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace” mun karbi wannan mummunan labari na rasuwar mashahurin malami, limami, jagoran al’umma, kazalika mai kokarin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin jama’a”.

Gwamnan yacigaba da cewa” Malamin mutum ne mai magana daya wanda yayi rayuwa abar koyi ga kowa, mutuwarsa zata bar wani babban gibi mai wuyar cikewa”.

“Amadadin gwamnati da al’ummar Kano, Ina mika ta’aziyyata, za Kuma mu cigaba da addu’ar Allah SWA yasa Aljannah Firdausi ce makomarsa”.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories