Thursday, April 30, 2026
HomeDa dumi dumiHukumar Kwastam ta Ƙaryata wata Sanarwa ta Bogi kan Ɗaukar Ma’aikata

Hukumar Kwastam ta Ƙaryata wata Sanarwa ta Bogi kan Ɗaukar Ma’aikata

Date:

Hukumar Kwastam ta Kasa ta nesanta kanta daga wata sanarwa da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa an fitar da jerin sunayen wadanda suka kai matakin karshe na daukar ma’aikata na shekarar 2025.

A cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar, ta ce labarin da ake yadawa bai fito daga Hukumar ba, kuma ba daga kowace tashar sadarwa ta hukuma da aka amince da ita ba.

Ta ce jama’a musamman masu neman aiki a hukumar su yi watsi da wannan labari domin ba shi da tushe.

Hukumar ta bayyana cewa tsarin daukar ma’aikata na bana ya fara ne da tallan hukuma da aka wallafa a ranar 27 ga watan Disamba, 2024, wanda ya jawo aikace-aikace sama da rabin miliyan daga masu neman aiki a rukunan Superintendent, Inspectorate, da Customs Assistant.

Bayan an kammala binciken takardu, an fitar da jerin sunayen mutane 286,697 da aka gayyata domin jarabawar kwamfuta (CBT) ta farko da aka gudanar a rukuni-rukuni don tabbatar da adalci da inganci.

Sai dai hukumar ta ce daga cikin wadannan rukuni, masu neman aiki na Superintendent Cadre ne kadai aka zaba domin cigaba da zuwa mataki na biyu na jarabawar.

An ce jarabawar ta biyu za ta gudana ne a cibiyoyi da aka ware a dukkan yankuna shida na kasar, bisa la’akari da jiharsu ta asali, a wani mataki na tabbatar da gaskiya, cancanta da hadin kai a tsarin daukar ma’aikata.

Sanarwar ta ƙara jaddada cewa duk wani sahihin bayani game da ɗaukar ma’aikata ana wallafawa ne kai tsaye a shafin updates.customs.gov.ng, tare da gargadin jama’a da su guji yada ko amincewa da bayanan da ba su da tabbas.

Haka zalika, Hukumar ta kuma tabbatar da cewa tana gudanar da ɗaukar ma’aikata cikin gaskiya da adalci, daidai da ka’idojin duniya da tsarin adalcin yankuna na Tarayya.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories