Jarumin Wasan Hausa na Masana’antar KannyWood, Adam A. Zango, ya fitar da wani fai-fan bidiyo – inda yake bayani akan sakonnin da ya aikawa abokai da mabiyansa, domin su ba shi tallafin Kudin da zai ci Kaji da sauran bukatu.
A cikin bidiyon, Jarumin, ya yi bayani cewar sakon neman taimakon da ya nema, ba wai ya tura shi ne ga kowa ba, sai dai ya aike shi ne ga mutanen da yake da alaka da su, da kuma masoyansa.
“Duk wanda ya ga ta WhatsApp number di na, ni na tura. Da kai na, na tura ba wani ba ne. Ni ne na sa account number ta, na dora – sabida haka a tura kawai domin na ci Kaji, na dan yi abubawa kawai.
A. Zango ya nemi mutane su yi masa addu’a Allah Ya sa Kajin da zai saya da Kudin su yi masa amfani.
Ku bi wannan sadau (link) din, domin kallon wannan bidiyo: https://fb.watch/m8Kq3-3TnJ/?mibextid=NnVzG8&startTimeMs=25772