Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaJami'an Tsaro Sun Hana Sanata Natasha Shiga Majalisa

Jami’an Tsaro Sun Hana Sanata Natasha Shiga Majalisa

Date:

Jami’an Tsaro Sun Hana Sanata Natasha Shiga Majalisa

A ranar Talata ne jami’an tsaro suka hana jerin gwanon motocin sanata Natasha Akpoti-Uduaghan shiga zauren majalisar tarayya, lamarin da ya sa ta sauka daga motarta ta taka ta shiga harabar majalisar tare da wasu magoya bayanta.

Sanatar wadda aka dakatar da ita na watanni shida ta yi niyyar komawa bakin aiki yau Talata – bayan kotu ta umarci majalisar ta mayar da ita.

BBC ta rawaito cewa, lokacin da motarta ta isa majalisar, jami’an tsaro sun hana ta wucewa abin da ya janyo ce-ce-ku-ce yayin da magoya bayanta suka fara ihu suna ƙoƙarin kutsawa zuwa cikin majalisar.

A ranar litinin ne dai Natasha ta sanar a shafinta cewa zata dawo majalisar ranar talata, shugabancin majalisar dai baice uffan ba kan wannan dambarwa.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories