Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kaddamar da shirin B’Odogwu, sabon Tsarin Gudanarwar Kwastam Mai Haɗaka, wanda aka fara da gwaji a tashar jiragen ruwa ta Port & Terminal Multi-Services Limited (PTML) da ke Legas.
Yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida a shiyyar PTML a ranar Laraba, 23 ga Oktoba 2024, Babban Kwamturola janar na Kwastam , Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa wannan tsari mai fasaha yana wakiltar wani muhimmin mataki a ci gaban zamanantar da aikin kwastam na Najeriya, wanda ya dace da mafi kyawun matakan duniya.
Kalaman sa, “B’Odogwu shi ne sabon tsarinmu na gudanarwar kwastam wanda ke kunshe da burinmu na yin ayyukan kwastam ba tare da takardu ba, wanda zai saukaka harkokin ciniki cikin sauƙi yayin da yake kiyaye matakan tsaro masu ƙarfi.”
“Ya kamata a lura cewa B’Odogwu zai maye gurbin Tsarin Bayanan Kwastam na Najeriya (NICIS II) a matsayin tsohon tsarin NCS. An samar da wannan tsarin ne da hangen nesa, tare da la’akari da cewa budadden tsari na bai daya na Ƙasa zai zo nan ba da jimawa ba, kuma B’Odogwu zai haɗu da shi idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da shi,” inji shi.
Ya bayyana cewa wannan shirin yana samun cikakken goyon baya daga tsarin doka da aka tanada a Dokar Hukumar Kwastam ta Najeriya ta 2023.
“Musamman, sashe na 28 da 29 na dokar sun baiwa hukumar damar samarwa, kula da kuma amfani da tsarin lantarki yayin da suke tabbatar da gaskiya da shawarar masu ruwa da tsaki.”
A cikin jawabin sa na gaba, CGC ya bukaci masu ruwa da tsaki da su rungumi wannan sauyi da fata na alheri tare da samar da ra’ayoyi masu gina jiki da za su taimaka wajen inganta tsarin.
“Yayin da muke fara wannan gwaji, ina kira ga duk masu ruwa da tsaki da su rungumi wannan sauyi da fata mai kyau tare da samar da ra’ayoyi masu kyau da za su taimaka wajen ƙara inganta tsarin, domin ra’ayinku yana da matukar muhimmanci ga nasarar wannan shiri.”
“B’Odogwu zai inganta ikonmu na saukaka ayyukan kasuwanci daga farkon aiki har zuwa karshe, ya ba masu ruwa da tsaki damar haɗawa da tsarin ta hanyar da aka kera musamman, ya goyi bayan yanke shawarar kasuwanci cikin sauri da hankali, kuma ya sauƙaƙe gudanar da harkokin kasuwanci.”
Babban kwanturolan ya gode wa masu gudanar da tashar jiragen ruwa, jami’an kwastam, dillalan kwastam masu lasisi, da kuma ƙungiyar aikin gyaran kasuwanci saboda goyon bayansu da sadaukarwarsu wajen ganin nasarar wannan shirin.
Ya umarci jami’an shiyyar PTML da su ɗauki horon da ya shafi wannan shirin da muhimmanci domin za su aiwatar da shi a wasu shalkwatoci. “Za ku zama shugabannin sauyi a Hukumar Kwastam ta Najeriya. Ana farawa a nan; za mu kula da shi har ya zama nasara a nan, kuma muna tabbatar muku cewa zai yi aiki.”
Ci gaban wannan tsarin haɗin gwiwa ne tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da tawagar shirin zamanantar da kasuwanci.