Madakin Kano ya Nada Maidattako Amatsayin Chiroman Yola
Anja hankalin al’umma dasu kasance masu da’a da girmama shugabanni tareda yawaita mika lamarin su ga Allah a duk lokacin da suka fuskanci wani kalubale na rayuwa.
Madakin Kano Alh Yusuf Ibrahim Cigari, shine yayi wannan kiran lokacin daya jagoranci biki nadin Alh Umar Faruk Muktar Mai Dattako amatsayin sabon Chiroman Yola.
Alh Yusuf Cigari, ya Kuma yi kira ga sabon Chiroman Yola daya kasance jakada nagari a duk inda yasamu kansa tareda kiyaye martabar gidansu, data Yolawa dama Masarautar kano baki daya.
Dayake jawabi Jim kadan bayan kammala nadashi, sabon Chiroman na Yola Alh Umar Faruk Muktar, ya godewa Madakin na Kano bisa ganin dacewar nadashi wannan sarauta tareda alkawarin zaiyi duk mai yiwuwa wajen kiyaye mutuncin Yolawa dama jihar kano a duk inda yake.
Bayan kammala nadin, sabon Chiroma yayi hawa zuwa gidansu inda ya zauna domin karbar gaisuwa daga ‘yan uwa da abokan arziki.
Bikin nadin ya samu halartar dubban mutane daga sassa daban daban na Nigeria harma da kasashen waje.