Rurum ya tallafawa daliban dake karatu a BUK su 100 da kudin makaranta naira dubu 50 kowannen su.
Wakilin Al’ummar Kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar wakilai ta kasa *Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum ya bada tallafin karatu ga daliban Yankin Kananan hukumomin guda uku dake karatu a jami’ar Bayero su 100.
Anyi bikin Mika tallafin ne ranar Laraba a Karamar Hukumar Rano, inda kowanne dalibi ya samu naira dubu 50 daga wakilin.
Cikin Wani jawabi mai dauke dasa hannun mataimakinsa na musamman kan Hulda da kafafen yada labarai Fatuhu Yusuf Bichi, Hon Kabiru Rurum Wanda ya samu wakilcin Alh Alhassan Abubakar Kibiya yace an baiwa daliban wannan tallafin ne domin rage musu wahalar da tsadar biyan kudin makaranta ta janyo.
Ya Kuma horesu dasu cigaba da Maida hankali a karatunsu domin Samun nasara a nan gaba, inda yasha alwashin cigaba da tallafawa bangaren na ilimi domin Samun al’umma ingantacciya.