A wata hira da akayi da Janar Manaja na tsarin zamanantar da kasuwanci mai taken TMP, Ahmad Ogunshola, tun a ranar Talata 4 ga watan Yuni na 2024, ya bayyana fatan cewa tsarin zamanantarwa da aka fito da shi zai taimakawa Najeriya mussaman a fannin tattara kudaden shiga da kuma baiwa dukiyoyin ‘yan kasuwa cikakkiyar kariya tun daga sauka, har isar su wuraren ma su kayan.
A yayin ziyarar manema kabarai a ofishin jami’an shirin a birnin tarayya Abuja, Ahmad ya ce ” Shirin zai samar da harajin Dala Biliyan 250 ga gwamnatin tsawon lokacin da aka dibar masa”.
Acewarsa, shirin ya riki babbar damar habbaka tattara kudaden shiga ta hanyar amfani da fasahar zamani “Wanda hakan zai zama mai Alfanu ga Gwamnatin tarayya”.
Shirin na TMP zai hada da shigar da ayyukan kasuwanci na hukumar hana fasa kwauri ta kasa da kuma bunkasa abinda masu ruwa da tsaki ke koya a fannin hada hadar kasuwanci. Hakan zai hada da bin hanyoyin samun amincewa wajen shige da ficen kayayyaki da biyan kudin harajin shigo da kaya da kuma sakin kayan.
Ya bayyana cewa shirin na zamanantarwar zai matso da Najeriya kusa a fannin hada hadar kasuwancin duniya ta hanyar amfani da fasahar zamani. Haka kuma shirin zai tallafawa kudurin gwamnati na bunkasa tattalin arziki ta hanyar saukaka kasuwancin kasa da kasa.
Ogunshola yayi bayanin cewa aiwatar da dukkan shirin na TMP zai shafi dukkan ayyukan hukumar Kwastom, ciki har da karbar haraji da tantance kayayyaki da kokarin yaki da fasa kwauri.
Da yake jawabi ga manema labarai, mai magana da yawun hukumar hana fasa kwauri ta kasa, CSC Abdullahi Maiwada ya ce ziyarar an yita ne domin yiwa al’umma jawabi kan ci gaban da aka samu daga tsarin na TMP wanda aka fara tsawon shekaru domin kula al’amuran kasuwanci.
Hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta hada kai da shirin domin samar da na’urar tantance madaukai wacce zata iya tantance madaukai 200 cikin awa guda. Wannan tsari karkashin jagorancin babban konturola janar, Adewale Adeniyi an yi shi ne domin rage lokacin tantance madaukan kaya.
“Abin da ake son cimmawa shi ne zamanantar da dukkan hanyoyon da mayar da ita mafi sauki da gamsarwa”, inji Ogunshola. Shirin dai ana yinsa a rukunin gidaje na hukumar kwastom dake Abuja wanda ya baiwa kwararru a fannin fasahar sadarwa damar samar da tsarin hada hadar kudi ma shige da ficen kaya.
Tsarin da aka dibarwa shekaru 20 ya kasu zuwa mataki 3
1. Mataki na 1(Shekaru daga 1 zuwa 6): samar da na’uara ciki har da na’urar zahiri da na fasahar zamami.
2. Mataki na(Daga shekara 7 zuwa 13):Kula da tsarin shirin da maye gurbin na’urori da ake bukata.
3. Mataki na (Shekaru 14 zuwa 20) mayar da tsrain zuwa ga jami’an hukumar kwastom tare da tallafin shirin na TMP wajen basu horo.
Da yake karin bayani, CSC, Usman Abba yayi bayyana irin alfanun shirin wanda zai baiwa masu shigo da kaya damar ganin yadda ake tantance kayan. ” Tsarin zai bada damar bibiya a kan lokaci da rage ayyukan barna”, inji Abdullahi Maiwada jami’in hulda da jama’a na hukumar Kwastom.
Wannan ci gaban na fasahar zamani anasa rai zai bunkasa tashoshin ruwan Najeriya wajen gamsasshen aiki da kuma yin kafada da kafada da tsarin da duniya ke kai a yanzu.