Sunday, October 25, 2026
HomeƘasashen ƘetareTsohon Shugaban Nijer Bazoum zai fuskanci shari'a kan cin amanar kasa

Tsohon Shugaban Nijer Bazoum zai fuskanci shari’a kan cin amanar kasa

Date:

Tsohon Shugaban Nijer Bazoum zai fuskanci shari’a kan cin amanar kasa


Sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula a jamhuriyar Nijer, sun bayyana aniyarsu ta gurfanar da shugaban farar hular da suka hambarar Mohammed Bazoum a gaban kotu, dangane da batutuwan da suka shafi cin amanar kasar da ke fiuskantar barazanar kai mata harin sojin kungiyar ECOWAS, domin sake tabbatar da maido da aiki da kundin tsarin mulki.


Bayan wani zaman taron da gwamnatin sojin ta gudanar a ranar lahadin, sun bayyana cewa, su na da cikakkun shaidun da za su gabatarwa kotunan kasar, da na duniya, da ke nuna cewa, hambararen shugaban kasar da makaraban siyasarsa na ciki da waje, sun aikata miyagun laifukan cin amanar ciki da wajen kasar ta Nijer, kamar yadda colonel-major Amadou Abdramane, daya daga cikin mambobin sojojin da ke mulki, ya bayyana ta kafar talabijin din gwamnatin kasar.

Ya ce gwamnati ta tabbatar da zarginta ne bisa dogaro da tattaunawar da shugaba Bazum ya yi da wasu ‘yan kasar da kuma kasashen ketare, da kumawakilan kasashen duniya ne daga inda ake tsare da shi.

Bazoum Mohammed dai ya tattauna da wakilan kasashen duniya aminan kasar Nijer, kafin yi masa juyin mulkin, kasshen da suka hada da Amurka da wasu daga cikin makarabansa na siyasa.

Ana dai ci gaba da tsare Muhammed Bazoum ne a fadar shugabancin kasar, tun bayan juyin mulki na ranar 26 ga watan yulin da ya gabata tare da dansa da matarsa, inda ya shaidawa kafofin yada labaran duniya da dama cewa, garkuwa sojojin suka yi da shi, inda suka barshi babu wutar lantarki, tare da barinsa daga shinkafa sai tuwon laushi kawai.

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ta aike da wakilai domin tattaunawa da jagororin juyin mulkin na Nijer akan yiwuwar sakin Muhammed Bazoum, na baya bayan nan sune Malaman addinin Islama daga Najeriya da kuma tsohon Sarkin Kano Muhammad Sunusi na biyu.

To sai dai hakan bata cimma ruwa ba, duk da cewar sun amince da zama kan teburin sulhu da ECOWAS.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories