Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kano ta gayyaci tsohon Gwamna Ganduje
Hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta kano PCACC, ta gayyaci tsohon Gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje domin bayyana gabanta don amsa wasu tambayoyi da kare kansa kan batun fefan bidiyon Dala.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, shugaban hukumar Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace suna sa ran bayyanar tsohon Gwamnan gaban hukumar a mako mai zuwa.
Muhyi yace, abinda yahana abinciki tsohon Gwamnan tun abaya hakan nada alaka da rigar kariya da yake da ita lokacin dayake Gwamna wanda hakan yasa baza’a iya gurfanar da shiba.
Tun a shekarar 2018 ne dai wani fefan bidiyo ya bulla da ake zargin tsohon Gwamna Ganduje na karbar kudaden kasashen waje, zargin da Ganduje da makusantansa sukasha musawa.
Wasu dai na ganin dawo da wannan batu nada alaka da siyasa domin kawo cikas ga kokarin tsohon Gwamnan na samun kujerar minista a sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, zargin da hukumar ta musanta.