Thursday, April 30, 2026
HomeLabaraiGamayyar kungiyoyin kwararru na kwankwasiyya sunyi Barazanar Daukar Matakin shari'a kan Tsohon...

Gamayyar kungiyoyin kwararru na kwankwasiyya sunyi Barazanar Daukar Matakin shari’a kan Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Baffa Bichi

Date:

Gamayyar kungiyoyin kwararru na kwankwasiyya sunyi Barazanar Daukar Matakin shari’a kan Tsohon Sakataren Gwamnatin Kano Baffa Bichi


Gamayyar kungiyoyin kwararru na kwankwasiyya (Kwankwasiyya Professionals) sunyi barazanar daukar matakin shari’a kan tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Dr Abdullahi Baffa Bichi, bisa abinda suka kira kalaman batanci da yayi ga tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai mai dauke dasa hannun shugaban hadakar kungiyoyin Comrade Haruna Musa Gaza, kungiyar tayi Alla wadai da kalaman na Dr Bichi wadanda tace wani yunkuri ne na tayar da zaune tsaye tareda bata kyakkyawan sunan da Sanata Kwankwason ya kafa tsahon shekaru.

Kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga tsohon Gwamnan na Kano wanda ta bayyana amatsayin Jagora abin koyi wanda kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma.

Kungiyar ta bukaci Dr Abdullahi Baffa Bichi daya janye kalamansa tareda neman yafiyar Kwankwaso.

“Mun bukaci Ab Baffa Bichi daya janye kalamansa, sannan yafito fili ya nemi afuwar Dr Rabiu Musa Kwankwaso cikin kankanin lokaci.

Gaza yin hakan, bamu da wani zabi daya wuce daukar duk wasu matakai da doka ta amince dasu na shari’a” inji Comrade Haruna Gaza.

An dai jiyo tsohon Sakataren gwamnatin na wasu kalamai na zargi da yayi na wasu makudan kudade da yayi ikirarin ana baiwa Engr Rabiu Kwankwaso daga lalitar gwamnatin kano, kalaman da suka janyo mahawara a tsakanin al’umma.

Release /AAS

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories