Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaAmfani da soson katifa da yashi yasa muka rushe shatale talen gidan...

Amfani da soson katifa da yashi yasa muka rushe shatale talen gidan gwamnati

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilanta na rushe shatale talen gidan gwamnati..

Gwamnatin jihar Kano tace akwai dalilai da dama da suka sanyata rushe shatale talen gidan gwamnati.

Gwamnatin Kanon Cikin wata sanarwa data fitar ta hannun mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa, tace sai da tanemi shawarar kwararru kafin daukar wannan mataki.

Sanarwar ta cigaba da cewa, kasancewar ginin bai cika ka’idojin kwararru afannin gine gine ba yasanya akwai yiwuwar zai iya faduwa tsakanin shekarar 2023 da 2024.

Sanarwar ta Kara da cewa, anyi shatale talen ne da soson katifa wanda aka gama amfani dashi, da kuma yashi da akai amfani dashi mai yawa amaimakon siminti.

Har ila yau acewar gwamnatin, “ginin yayi tsayin da za’a barshi agaban gidan gwamnati ta la’akari da yadda yatare babbar kofar shiga gidan.”

Bugu da kari acewar sanarwar, “yana janyo cinkoson ababen hawa saboda girmansa.”

Rushe shatale talen dai ya janyo suka daga bangarori daban musamman wadanda ke ganin cewa da gangan gwamnatin takeyi kawai dalilai ne na siyasa.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories