An Cika Kwanaki 100 da Mutuwar ‘Yan Wasan Kano 22
An gargadi iyaye da ‘yan uwan matasa ‘yan asalin jihar kano da suka rasa rayukansu akan hanyarsu ta dawowa daga Jihar Ogun inda akayi gasar wasanni ta kasa, dasuji tsoron Allah wajen kiyaye dukiyar marayun dake hannayen su.
Mai rikon Kujerar shugabancin hukumar wasanni ta jihar kano Alh Ibrahim Umar Fagge shine yayi wannan gargadi lokacin da aka gabatar da taron Addu’ar cika kwanaki dari(100) da rasuwar ‘yan wasan kano 22 da suka rasa rayukansu awani mummunan hadarin mota a garin Kura akan hanyarsu ta dawowa gida bayan samun nasara a gasar wasanni ta kasa (National Sports Festival) da akayi a jihar Ogun a watan Mayun daya gabata.
“Cin kudin marayu mummunan laifi ne agurin Allah Subhanahu Wata’ala inda yayi tanadin azaba mai radadi ga duk wanda yaci kudin marayu”.
Ibrahim Fagge yakara da cewa, kamata yayi ayi amfani da kudaden da aka samu tallafi daga gwamnati da daidaikun al’umma wajen inganta rayuwar magadan da aka bari batareda sun shiga wani hali na kakani kayi ba.
Dayake karin haske kan irin tallafin da suka samu, Mal Abdullahi Baffa Bature ya bayyana cewa izuwa yanzu kowane mamaci ya samu sama da Naira miliyan 8 inda ake dakon tallafin da gwamnatin jihar kano tayi alkawari na Naira miliyan 6 ga kowane mamaci.
An daiyi taron Addu’ar ne a harabar hedikwatar hukumar wasanni ta jihar kano.