Thursday, April 30, 2026
HomeKotuBabbar Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da yunkurin rushe shaguna a...

Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da yunkurin rushe shaguna a kantin kwari

Date:

Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da yunkurin rushe shaguna a kantin kwari


Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Kano karkashin jagorancin Justice A M Liman, ta amince da dakatarwa ta wucin gadi akan yunkurin gwamnatin Kano na rushe wasu gine gine a kasuwar Kantin Kwari.

Wannan dai ya biyo bayan wata kara da wani Alh Abdurrahman Ahmad yashigar gaban kotun inda yake karar gwamnan Kano da kwamishinan shari’a na Kano, da gwamnatin Kano, da Ma’aikatar filaye da hukumar tsara birane da kuma rundunar ‘yansanda.

Sauran wadanda ake karar sun hadarda, babban sufetan ‘Yansanda na kasa, da kwamishinan ‘yansandan Kano, da hukumar Civil Defense da babban kwamandan Civil Defense na kasa da kuma kwamandan hukumar a Kano.

Alh Ahmad wanda yashigar da wancen koke gaban kotun, na neman kotun ta hana wadancen hukumomi da jami’an gwamnati yunkurin rushe masa shaguna dake a gini mai lamba 49 da suka hadarda T57, T124 da kuma T125 dake a hawa na daya dana biyu na wannan gini wanda yake a tsohon ginin ‘Yan tebura Mall.

Tuni dai kotun ta amince da rokon daya shigar gabanta inda ta bukaci a sadar da wadanda abin yashafa da umarnin nata har zuwa lokacin da zata saurari cikakkiyar shari’ar.

A kwanakin bayane dai gwamnatin Kano ta shafa Jan fenti a wasu shaguna dake kasuwar Kantin Kwari, alamar dake nuna cewa za’a rushe gine ginen.

Kafin wannan madai, gwamnatin ta sanya alamar ta Jan fenti a gine gine dake kan titin zuwa Jami’ar Bayero, abinda yasanya mamallaka gine gine garzayawa gaban kotun.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories