Bazamu lamunci Yarfe da Bata suna ba~~ Babbar Kotun Jihar Kano
Babbar kotun Jihar kano tace bazata lamunci kazafi da bata sunanta dana ayyukan taba, inda tace zata dauki tsauraran matakai Kan duk wani dake da nufin yin karan tsaye ga ayyukan shari’a a fadin jihar kano.
Babbar kotun na wannan gargadi ne biyo bayan wani faifan bidiyo dake yawo a kafafen sadarwa dake nuna wani mutum mai suna Sirajo Isa Yarima na kalubalantar hukuncin da wata babbar kotun kano ta yanke nayin gwanjon gidansa sakamakon gaza biyan bashin da ake binsa, inda yake zargin anyi masa rashin adalci.
Babbar kotun ta bakin mai magana da yawun kotunan jihar kano Baba Jibo Ibrahim, tace anbi duk wasu ka’idoji na shari’a kafin kaiwa ga yanke wancen hukunci gamida bashi dama ta kare Kai wanda bai taba halartar zaman shari’ar ba.
Kotun ta kara da cewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nigeria yabada dama duk wanda wani hukunci bai masa ba yanada damar daukaka kara domin kalubalantar hukuncin, to amma acewar kotun shi wancen mutum bai daukaka kara ba amma sai ya bige da kokarin bata suna abinda kotun tace bazata lamunta ba.
Idan za’a Iya tunawa babbar kotun Jihar kano karkashin jagorancin Justice Maryam Ahmad Sabo ta saurari wata kara da aka shigar gabanta kan biyan bashi wanda bayan baiwa kowane bangare dama tareda tabbatar dame laifi, kotun ta yanke hukuncin sayar da gidan wanda ake zargi domin biyan bashin da ake binsa bayanda aka kasa samun wata kadara da za’a siyar abiya bashin.
Maimakon daukar mataki na gaba na daukaka kara, wanda ake karar ya fito kafafen sada zumunta da kalamai na batanci ga kotun yana me zargin anyi masa ba dai dai ba, abinda yasanya kotun fitar da wannan sanarwa.