Daga: Abdulsalam Mahmud
Mafiya yawan Kasashe a duniya yanzu haka suna fama da kalubalen koma baya ta fuskar tattara Haraji, Kuma Najeriya itama ba’a bar ta a baya ba, wajen fuskantar wannan kalubale na samun koma baya wajen samun kudaden shiga.
Duba da yanayin da ake ciki a kasar na karancin kudaden shiga, da matsin tattalin arziki ya sanya Gwamnatin Tarayya kaddamar da wani shiri na musamman mai tsawon wa’adin shekaru biyu, don zamanantar da ayyukan hukumar hana fasa qwauri ta kasa Kwastom.
Manufar samar da shirin ita ce domin yin duk mai yiwuwa wajen samar da sauyi ga ɓangare ko yadda ake tattara haraji a kasar nan, a kokarin gwamnati na ganin an rage yawan dogara aka man fetur d arzikin dake bangare.
Gundarin abun da ake fatan cimma karkashin shirin sune samar da sauyi mai ma’ana ga yadda hukumar Kwastom ke tattara haraji a kasar, bunkasa bangaren kasuwancin kasar ta hanyar samar da yanayi mai kyau musamman ga masu zuba jari, da kuma dakile ayyukan cin hanci a bangaren Tattara kudaden shigar.
Ana Aiwatar da shirin ne karkashin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kan su wanda ake kira PPP, Inda aka cimma yarjejeniyar jinginarwa a ranar 30 ga watan Mayu na shekarar 2022, tsakanin gwamnatin tarayya ta hanyar hukumar Kwastom da kamfanin dake kula da shirin TMP a matsayin wanda aka jinginarwa.
Kari kan ci gaban fasahar zamani da samar da na’urori na fasaha, kamfanin dake kula da shirin zai taimakawa ayyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa ciki har da kula da na’urorin da horar da jami’anta daga ranar da aka fara aiwatar da shirin har zuwa shekaru 20 na jinginarwa da aka tsara.
Ribar dake tattare da wannan shiri
Ana fatan cimma nasarori da dama karkashin wannan shiri, da suka hadar da:
1. Bunkasa bangaren samun kudin shigar gwamnatin tarayya, ta hanyar amfani da dabarun zamani da kawar da kofofin zirarewar kudaden shigar ga gwamnatin tarayya.
2. Zamanantar da bangaren fasahar zamani na hukumar Kwastom don samun yanayi ingantacce wajen gudanar da kasuwancin zamanin.
3. Aiwatar da wasu dabaru da zasu taimaka wajen dakile fasa qwaurin kayayyaki, ta hanyar hada qwiwa da hukumomin dake da jiɓi da hakan.
4. Samar da tsarin bibiyar motsin kayayyaki na zamani, masu shigowa da wadanda za a fitar ko ta kasa ko ruwa ko kuma sama.
5. Samar da dabarun saukaka aikin da rage yawan mutanen dake shiga a dama da su, wato na’urori su wadata don saukaka kashe kudin tafiyarsa da dakile cin hanci da rashawa.
6. Shirya taron karawa juna sani ga jami’an hukumar Kwastom da sauran wadanda suka yi haɗaka kan wannan shiri.
Ribar shirin ga Najeriya
Shirin yana fatan bunkasa bangaren samun kudin shiga ga gwamnatin tarayya, tare da kokarin ganin an iya hada Dala Biliyan 250, tsawon lokacin jinginarwar.
Kazalika daɗi kan hakan, shi ne kokarin sanya Najeriya a sahun farko a duniya, ta fuskar kasashe masu takama da fasahar zamani wajen gudanar da kasuwanci a matakin duniya, da kuma taimakawa kasuwancin kasa da ƙasa tsakanin Najeriya da abokan cinikayyarta.
Ta Ya ya wannan shiri zai taimaki Bangaren Samun Kudin Shigar gwamnatin tarayya?
Amfani da fasahar zamani wajen Zamanantar da ayyukan hukumar Kwastom, babbar hanya ce ta bunkasa harajin da ake samu, kuma da dakile duk wata lam’a dake tattare da tara haraji.
Shin Tsarin Jinginarwa ce hanya mafi kyau wajen cimma burin da ake fata?
Kusan ana ganin ba laifi bane a harkar kasuwanci damka wuka da Nama a hannun wanda ya fika sanin karatun yanka, ko ba komai hakan zai taimsks wajen tsara abubuwan ci gaba da bangaren yake hange zai fi taimakawa domin kaiwa ga ci.
Shin Wannan shiri zai zama Silar wasu su rasa aikinsu?
Masu wannan hasashe ya kamata su daina, domin kuwa wannan shiri an tsara shi ne da nufin ƙirƙirar sabbin damarmakin ayyukan yi ga al’umma, saboda samar da damar aiki ga al’umma ce hanyar da zata karfafi duk wani kasuwanci a duniya domin bunkasarsa.
Jawabin Rufe wa
Shirin Zamanantar da ayyukan hukumar Kwastom, shiri ne mai takaitaccen lokaci da aka ware, da nufin sake fasalin ayyukan hukumar domin tafiya da zamani, ta hanyar amfani da sabbin dabarun da zamani ya fito da su, kuma shirin zai matukar tallafawa gwamnatin tarayya, domin dole ta yi tunkaho da shi a cikin jerin Ayyukan ta.
Mahmud, Deputy Editor Of PRNigeria contributed to this Article. Contact babasalam1989@gmail.com