*Daukata Da Karfi Da Yaji Daga Gidana, Tsare Ni, Da Kulle Ni A Gidan Yarin Kuje*
_Farfesa Usman Yusuf
12 Fabrairu 2025_
*Gwamnati Tasa Hukumomin Tsaro Su Sa Mani Ido*
Sai da jikina ya ba ni cewa gwamnati ta soma bibiyata tun daga lokacin da na soma fitowa fili ina sukar tsare-tsaren gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da suka zama wa `yan Nijeriya wata bakar ukuba. Na san cewa tabbas hukumomin tsaro a sarari da kuma ta hanyar laturonik suna bibiyar iyalaina da ni kamar yadda wannan gwamnati ta ba da umarni.
*Abu Na Karshe Da Ya Tayar Musu Da Hankali: Taron Matasa a Bauci*
A ranar Asabar 25 ga watan Janairu na shekarar 2025, aka gayyace ni Bauci domin shugabantar taro na farko na Tafiyar Matasan Arewa wacce kungiya ce ta gwagwarmaya ta matasan Arewa wacce take da rassa a duka jihohi 19 na Arewacin Nijeriya. Taken taron shi ne gudunmawar matasa ga gina kasa.
Yawancin wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun yi ne da Hausa, sai dai na yi bayani cikin harshen Hausa da na Ingilishi domin kai wa ga dinbin masu saurare. Na yi kira ga matasa su farka daga bacci su dau ragamar rayuwarsu a hannunsu saboda a tarihi, matasa ne suke gina kasashe, ba tsofaffi ba. Na yi magana a kan wadannan batutuwa guda 10 da suke biye:
1. Babu wanda Arewacin Nijeriya za ta zarga illa kanta a game da bakar azabar da wannan gwamnatin take gana wa jama`ar Arewa duk da Arewar ce ta ba shi kuri`a kashi 62 cikin kashi 100 da ta sa gwamnatin ta ci zaben.
2. Tikitin Musulmi-Musulmi da Jam`iyyar APC da ke mulki ta yi amfani da shi a zabukan Shugaban Kasa a 2023 yaudara ce da aka yi amfani da ita domin kara haddasa kiyayya tsakanin Musulmi da Kiristoci da ke yankin.
3. Akwai dadadden shiri na farraka kan mutane Arewa ta amfani da matsalar tsaro (Boko Haram, da `Yan Fashin Daji, da Lakurawa, da sauransu.), iza wutar rikici tsakanin Hausawa da Fulani da ke Arewa Maso Yammacin kasar nan, da kuma tsakanin Fulani da sauran kungiyoyin kabilu da ke sauran sassan yankin. Amfani da tikitin Musulmi-Musulmi da Jam`iyya mai mulki ta yi ya kara kawo rarrabuwar kai na addini da zaman rashin yarda da juna.
4. Matsalar tsaro da ta tsananta ta wargaza yankin tare da ruguza zamantakewarta, ya sa ta kara talaucewa, ga yunwa da kuma zama mai hadarin gaske.
5. Ruguza tsarin masarautu da ake matukar mutuntawa a yankin, da wulakanta su kamar yadda aka yi a johohin Kano da Adamawa.
6. Rashawa da kuma yadda gwamnati ta ke amfani da wasu masu wa`azi da ke yankin, su ci gaba da lallashin talakawa da ke fama da bakar wahala.
7. A yanzu haka wannan gwamnatin tana daukar nauyin Hausawa makada da mawaka na `yan siyasa suna buga ganga da wakoki na haddasa gaba da kiyayya tsakanin mutanen Arewacin Nijeriya da `yan uwansu da ke Jumhuriyar Nijar.
8. Tabarbarewar dangantaka tsakanin Nijeriya da Jumhuriyar Nijar da kuma ficewar Mali da Burkina Faso da Nijar daga kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka wato ECOWAS, labari ne mara dadi ga tsaro, da zamantakewa, da tattalin arzikin Nijeriya musamman Arewacin Nijeriya.
9. Kawance da Shugaban Kasa Tinubu ya kulla da Faransa babban abin damuwa ne ga tsaron Nijeriya da na Yammacin Afirka kuma manuniya ce ga abubuwa marasa dadin ji da za su auku nan gaba.
10. Akwai bukatar gwamnatin Shugaba Tinubu ta sake nazari da janye tsare-tsarenta na tattalin arziki da ke haddasa matsananciyar wahala ga `yan kasa.
A karshe, na yi kira ga matasan Arewa su ci gaba da hada kai, su kauce wa dukkan wani nau`i na tashin hankali da miyagun abubuwa ko laifuka, su shiga lamuran gina siyasa mai ma`ana, su bijire wa duk wani mutum ko kungiya da za su yi kokarin yin amfani da addini ko kabilanci domin raba kan mutanen yankin.
`Yan jarida da kafofin watsa labaru, da na yada labaru sun ta ba da labarin wannan taro babu kama hannun yaro.
Da yammacin wannan rana da aka yi wannan taro, na koma masaukina a otel da na sauka, sai na lura da wasu mutane baki a hanyar shigowa da kuma wajen cin abinci, dandanan na san cewa jami`an tsaro ne suke bi na.
*Kama ni da tsare ni tsawon kwana 6 a hannun hukumar EFCC*
A ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025 da wuraren karfe shida da rabi na almuru, ina shirin shan ruwa da buda baki, matata ta hawo wajena da ke gidan sama, ta sanar da ni cewa wasu mutane su biyu sanye da bakaken kwat sun kwankwasa kofa kuma sun shigo cikin gida, suna cewa na san da zuwan su.
Na sauko kasa sanye da jallabiya, ba hula, sanye da silifas, na same su, suka gabatar da kan su, cewa su jami`an hukumar EFCC ne da aka ba umarnin su dauke ni su kai ni shalkwatarsu.
Na tambaye su bajen su, suka nuna mun tare da neman in musu ahuwa saboda mantuwar da suka yi tun farko ba su nuna mun ba. na bukaci su nuna mun takardar shaidar an turo su ne su kama ni. Suka ce ba sa bukatar ko daya. Har ila yau na tambaye su dalilin da ya sa ba a aiko mun da wata takarda ta gayyata ba, aka zo aka mun wannan kutse. Daga nan na nemi su bari in koma sama in canza kayan da ke jikina, sai suka hana ni suka tare gabana. Har ila yau na nemi su bar mai daki na ta hau sama ta kawo mun tufafin da zan canza, suka yi kememe suka hana.
Muna fita daga gida na ga `yan sandan kwantar ta tarzoma su biyar rike da bindigogi, wasu an girke su a ta bayan gidana, wai su tare baya ko da zan iya bi ta kofar can baya ko ta tagar baya in tsere. Sun bar mota bas da suka zo da ita tana kunne, direbanta yana zaune a ciki.
Da musu ya yi zafi, sai mai daki na ta soma mayar da martani ga hargowar da jagoransu yake yi, da ya sa ta fada masa kalaman da suka harzuka shi da sauran ayarin nasa.
Diyata `yar shekara 14 ta firgita da wannan hali da ta lura ake ciki. Na mata magana don lallashe ta saboda sun tare hanyar da zan matsa kusa da ita in rungume ta in mata magana. Na bukaci mai daki na ta kira `yan uwana da lauyoyina don sanar da su.
Jagoran su, ya fusata ya kwace wayata daga hannuna, ya ciccibe ni ya sa ni a cikin bas din, ya zaunar da ni a tsakaninsa da `yan sandan mai bindiga.
Daga nan direban ya fisgi motar a guje, yana tukin ganganci, wani lokaci ya yi wasa da motar har a wuraren ba da hannu har suka kai ni shalkwatar hukumar EFCC. Sai ka ga yadda duka jami`an da ke sanye da bakaken kwat da `yan sandan kwantar da tarzoman su biyar rike da bindigogi suke ta doki da nuna sun cika aiki kai ka ce sun kamo Kachalla Bello Turji ne, rikakken dan fashin dajin nan da ya addabi Zamfara.
Ya kamata mu san cewa babban dalilin wannan wawanci na EFCC shi ne anfani da karfin gwamnati wajen cin zarafi da tursasa wa iyalina saboda ina fadin gaskiya. Ni a wajena, ba wata bajinta ko burgewa ba ce aka yi, kuma ko gezau ba zan yi ba, da wannan abin kunya da aka aikata gare ni.
Muna isa EFCC, aka sallami `yan sandan su biyar da dafa musu baya irin ta jinjina musu saboda kokarin da suka yi, ni kuma jami`an da ke sanye da kwat din suka raka ni sama inda ofishin shugaban sashen yaki da laifuka na zamba a sayen kaya (PFS) a takaice, na gabatar masa da kaina na kuma tambaye shi dalilin da ya sa ya aike da jami`ansa suka dauko ni da karfi da yaji daga gidana zuwa ofishinsa. Sai ya mika mun wasu takardu ya ce su ne tuhume-tuhumen da ake mun, ya bukaci in sa hannu, na sa hannu bayan kwam-gaba-kwam-baya.
Na nemi ya ba ni ruwa in sha saboda azumi da na yi, ya ba ni ruwa, na nemi ya bari in kira mai dakita. Abin takaici wayata ta mutu saboda babu caji. Aka hana ni kiran waya don sanar da mai dakin tawa da diyata inda nake da kuma halin da nake ciki.
Bayan na sa hannu kuma na karbi kwafin tuhume-tuhumen da ake mun, shugaban na PFS wanda da alama sauri yake yi ya tashi aikin wannan rana, ya bukaci mataimakinsa ya kai masa jakarsa motarsa da ke kasa, kamar ni ne na karshe a jerin aikinsa na wannan rana.
Babu wanda ya fada mun dalilin kamo ni da karfi-da-yaji, ko za a tsare ni ko ba za a tsare ni ba, ko yaushe za a bari in ga iyalina da lauyoyina, ko yaushe za a gurfanar da ni a gaban kotu domin sauraron tuhume-tuhumen da aka kakaba mun.
Daga nan aka tafi da ni da kafa muka zagaya ainihin ginin zuwa inda ake tsare mutane. Bayan an kammala batun tsare ni, na bukaci a bari in yi sallar Magrib da Isha, bayan na idar aka kai ni inda za a tsare ni, inda aka tsare ni cikin wasu tsararru su uku.
Wadanda ake tsare da su da daman su musamman matasan sun gane ni kuma suka zo suka gaishe ni, tare da mun addu`a da kyakkyawan alheri. Wadanda muke tsare taren suka yi matukar mutunta ni, mutuntawa irin wacce ake ba wanda aka gan shi da furfura. Suka ba ni ruwan leda na fiyawata da ruwan shayi mai zafi a kofi, da suka taimake ni samun saukin ciwon kan da yake damuna sakamakon raba ni da maganina ga kuma azumi da na yi tsawon sa`a 24.
Wadanda ake tsare da su sukan kwanta a wata `yar katifa mara girma mara kauri da ke taba juna a siminti. Abokan tsarewar suka ba ni damar in kwanta daidai kusa da jikin bango.
Da karfe goma sha dayan dare, aka kashe wuta, aka kulle kofofin inda ake tsare da mu da makulli ta waje. Na kwanta a cikin duhu, da jin zafin rashin magana da mai dakita da diyata domin sanar da su inda nake da kuma halin da nake ciki.
Ba a dade da kashe wutar ba abokan kwanciyata bacci ya kwashe su suka soma munshari da karfi, da zai iya hana ni rintsawa, amma haka baccin ya kwashe ni, karar bude kofofin inda muke tsare da masu gadin wajen suka yi domin mu fita mu yi Sallah da wuraren karfe biyar na asuba ta tada ni daga baccin. Muka yi sallah a adarkin da ke `yar hanyar shiga wajen.
A ranar Alhamis 30 ga watan Janairu na 2025 da karfe 7 na safiyar ranar aka kira sunana aka ce in shirya za a kai ni kotu da karfe 8 na safe. Ina fitowa daga ginin da wuraren tsare mutanen ke cikinsa tare da jami`in tuhumata (IO), an ajiye wani mai daukar hoto na sashen yada labaru na hukumar EFCC a inda zai dinga daukar hotona da gashina buzu-buzu, ina sanye da silifas ba hula sanye da dai kayan da aka dauko ni daga gidana jiya da almuru.
Lokacin na tabbata cewa daya daga cikin umarnin da aka ba hukumar EFCC shi ne a tozarta ni a idon duniya, da karya mun karfin gwiwa da zubar mun da mutunci ta kago wasu tuhume-tuhume.
Da na shiga bas din, sai cikin wasa na sanar da jami`an hukumar cewa sun fa manta ba su sa mun ankwa a hannu da mari a kafata da sarka a jikina ba. sai suka fashe da dariya suka ce haba “Haba Oga, e no reach dat level” wato Haba Oga ai ba ta kai ga haka ba.
Mai shari`a ta daga ranar da za a gurfanar da ni zuwa Litinin, 3 ga watan Fabrairu shekarar 2025, saboda lauyoyin hukumar EFCC ba su gama shiri ba tukuna, da ke nufin zan sake yi karin kwana hudu a tsare a dakin da ake tsare mutane na hukumar EFCC.
Muna dawowa EFCC, na tarar da mai dakita tana jirana da wasu tufafin da zan canza da abinci da ta daho daga gida; rabon da in ci wani abu kusan sa`a 40 kenan.
Na tuna mata cewa fada da muke yi ba da hukumar EFCC ko jami`anta muke yi ba, fada ne da gwamnatin rashawa da kama karya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Na lallashe ta, ta biyo ni zuwa sama domin ta ba jami`an hukumar da ta yi sa-in-sa da su a lokacin da suka zo gidanaj domin tafiya da ni jiya da almuru. Hakurin da ta ba su ya yi tasiri saboda an daga matsayina daga dakin da ake tsare da ni tare da mutane ukku, zuwa dakina ni kadai.
Iyalai da abokai da suke ta kai mun ziyara su suka debe mun kewa, inda mukan taka a dakalin wajen, ina karatun Alkur`ani, da samun wadataccen hutu da samun natsuwa daga fadi-tashin-da na saba yi a waje. Na samu natsuwa da kwanciyar hankalin da ban taba samu ba a rayuwata.
A ranar Litinin 3 ga watan Fabrairu da za a gurfanar da ni a gaban kotu, kotun ta cika makil da lauyoyi, da kungiyoyin matasa da `yan rajin kare hakkin jama`a. Bayan an gurfanar da ni, sai mai shari`a ta ba da umarni a tsare ni a gidan yari na Kuje sai 12 ga watan Fabrairu na shekarar nan, ranar da zata zarce hukunchi ko zata bada beli na.
Wannan ya kawo karshen kwana shidda da na yi a tsare a hannun hukumar EFCC, na fara zaman kwana tara a gidan yari na Kuje. Nan take jami`an hukumar EFCC suka dauke ni a motarsu bas, suka mika ni ga Hukumar Gyara Hali ta Nijeriya a gidan yarin Kuje.
*Kwanaki 9 na farko da na yi a tsare a Gidan Yari na Kuje*
Daga waje sunan Gidan Yari na Kuje, mutum yakan ji kamar za shi inda idan an je ba a dawowa ne. Abubuwan da na gani duk zama na a gidan ba haka bane. ma`aikatan wajen suna da tausayi da girmamawa da tallafawa da matukar nuna kwarewa da iya aiki wajen gudanar da aikinsu. Suna mutunta masu zaman gidan yari da yawancinsu matasa ne, da daukarsu a matsayin mutane da kuma nuna musu fahimta.
Bayan anyi abubuwan da suka wajaba aka kai ni sabon masaukina, da ake kira da suna segregation unit wato inda ake tsare da masu zaman gidan yari manya masu matsayi. Kodayake akwai `yan wasu abubuwa da aka tanadar na alfarma, gittawar da masu gadi ke yawan yi, da kamarorin da aka sanya a ko`ina suna kallon ciki da wajen gidan yarin, da ake kallo daga can shalkwata, da kuma yadda masu gadi suke kulle kofar kowanne wajen da ake tsare da mutane daga waje a kowacce rana da karfe 8 na dare, a bude washegari da karfe 7 na safe, wato sa`a wajen 11 a garkame cikin daki mai zafi da ke da fadin kafa 10 da kafa 6 da `yar taga guda daya tilo, su suke tuna wa mutum cewa ya rasa `yancinsa da walwalarsa.
Walwalar sa`a 13 a cikin harabar gidan yarin aba ce mai muhimmanci. Mutum zai iya tafiya zuwa masallaci da ke daya gefen gidan yarin domin yin Sallar Azahar da La`asar, salloli biyu kadai da ake yi a jam’i a masallacin saboda da karfe 6 na yamma ake kulle dakunan da ake tsare da mutane, a bude washegari da karfe 9 na safe.
Zama a Gidan Yari na Kuje ya sa na tuna da lokutan da nake makarantar kwana ta sakandare, inda fursunoni suka zama `yan sandan juna. Kowanne fursuna ya san aikin da aka ba shi da an bude shi da safe. Ana tsaftace harabar kuma ana mutunta juna tsakanin ma`aikatan gidan yarin da fursunoni.
Fursunonin suna nuna alamun sun san me yake aukuwa a cikin gari. Da yawansu sukan zo wajena suna kwantar mun da hankali da kalaman su. Suna gane ko ni wane ne, sai ana ta rokona in hadu da daidaikun jama`a da kungiyoyi da suke so in tsaya musu idan na fita, da alama sun mance da ni ma ina da tawa matsalar data kawo ni.
Ina zama da matasa da kuma ji daga matasan da ake zargi ko aka yanke musu hukunci saboda kasancewa `yan Boko Haram, ko `Yan fashin daji, ko IPOB, ko masu zanga-zanga `yan Shi`a, ko `yan fashi da makami, ko fataken miyagun kwayoyi, ko masu kisan kai, ko masu fyade, ko `yan damfara, ga su nan dai jerin laifukan ba adadi.
Har ila yau, na shiga asibitin gidan yarin domin ganawa da ma`aikatan asibitin da majinyata. Na je na tattauna da fursunonin da suke inda ake koya musu sana`o`i, da dan dakin karatu da babu littafai sosai da kuma ginin Budaddiyar Jami`a ta Nijeriya. Ban shiga dakunan da ake tsare da fursunoni ba, amma na kalle su suna buga kwallo.
Abin takaice ne da tausayi a ga matasa da suke cikin ganiyar kuruciyarsu, suna garkame a gidan yari. Abin da ya fi ciwo shi ne jin labarurrukan fursunoni da dama sun haura shekara 10 a tsare suna jiran a musu shari`a.
Gidan Yari na Kuje da aka tsara shi don fursunoni 560, a yanzu akwai dan Adam 960 inda 198 (kashi 21 cikin kashi 100) aka yankewa hukunci, sai 765 (Kashi 79 cikin kashi 100) suke jiran a yanke musu hukunci.
Na dauke kwanakin da na yi a Gidan Yari na Kuje a matsayin wata rahama da kuma ilimi da ba zan taba samu ba a dukkan wani aji. Wata dama ce ta saurare da ganin wahalhalu, da jarrabawa, da damuwa da wadannan matasa da wasu dattijai suke ciki.
Na yi alkawarin zan yi iya kokarina wajen ganin na kai ga jami`ai da hukumomi da za su iya taimakawa abubuwa su kyautatu.
*Karin wasu kwanaki 15 a tsare a Gidan Yari na Kuje*
Mun koma kotu Larabar 12 ga watan Fabrairu na 2025 domin mai shari`a ta saurari bukatar ba da belina daga lauyoyina. Sai mai shari`ar ba tare da bata Wani lokaci ba, ta dage sauraron yanke hukuncin za ta ba da belina ko a`a, zuwa ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairu, na 2025. Aka mayar da ni gidan yari domin in kara wasu kwanakin 15.
*Kammalawa*
Ina da cikakken yarda da kuma amincewa da ayarin lauyoyina da za su yi tsayin daka wajen ganin sun kare ni daga kage da karairayi marasa tushe da hukumar EFCC ta tuhume ni da su, da dukkansu na ce babu wanda na aikata.
Iyalina da ni kaina mun yi matukar kaduwa kuma muna matukar godiya da irin gagarumar goyon baya da muka samu daga mutane da suke duk sassan kasar nan da kuma kasashen ketare.
Ina so in tabbatar wa da dukkan `Yan Nijeriya cewa tsarin shugabanci na kama karya na gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taba sa ni gudu ko ja da baya ko sa ni in yi shiru ba. domin kuwa tsarin shugabanci ne da ke danne dukkan wata halaktacciyar adawa ga yadda yake gudanar da rashin iya mulkin kasarmu ta gado.
Ina kira ga dukkan `yan Nijeriya su bijire wa wannan lamari mai hadarin gaske da ya yi kama da na lokacin bakin mulkin da sojoji suka yi wa Nijeriya.
Ina godiya gare ku, Allah Ya yi wa kasarmu Nijeriya albarka Amin.
Usman Yusuf Farfesa ne bangaren cututtuka da sauran lalurori na jini, kuma Babban Likitan Dashen Bargo.