EFCC na binciken ministoci takwas na gwamnatin Buhari
Akalla ministoci takwas ne da sukayi aiki a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gayyata kan zarge zarge dakeda alaka da cin hanci da rashawa.
Majiyar DAILYFEEDSHAUSA ta bayyana cewa, an aike da takardun gayyatar ne ga tsoffin manyan jami’an gwamnatin domin suzo suyiwa hukumar bayani akan yadda suka kashe kudaden da aka tura ma’aikatunsu, da wasu ayyuka da ma’aikatunsu suka aiwatar.
Rahotanni sun bayyana cewa, an aike da wasikun ne tun kafin dakatar da Abdurrashid Bawa shugaban hukumar.
Hukumar ta EFCC acewar wata majiya, tuni ta ƙaddamar da bincike kan gwamnatin data gabata.
Majiyar ta Kara da cewa, bayaga tsohuwar ministar al’amuran mata Pauline Tallen da aka gayyata kan zargin batan wasu kudade Naira Biliyan biyu, an gayyaci wasu tsoffin ministoci bakwai.
Idan za’a iya tunawa, Sale Mamman tsohon Ministan lantarki zamanin tsohon shugaban kasa Buhari, ya fada komar hukumar kan zargin badakalar Naira Biliyan 22 dake da alaka da samar da wutar lantarki.