Gamayyar kungiyoyin masu ruwa da tsaki kan Ilimi ta yaba da matakin Gwamnatin Kano na rushe gine gine da akayi a makarantu
Gamayyar kungiyoyi masu ruwa da tsaki kan Ilimi a Jihar Kano ta yabawa gwamnatin jihar kan matakin data dauka na rushe gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba a makarantu.
Gamayyar kungiyoyin sun bayyana matsayin nasu ne a wani taron manema labarai daya gudana a Kwalejin fasaha ta Kano.
Dayake jawabi ga ‘yan Jarida amadadin gamayyar kungiyoyin, Dr Ibrahim Usman Aikawa, yace abune mara dadi adai dai lokacin da ake kokarin fadada makarantu domin gina ajujuwa da guraren bincike saiga wasu marasa kishin kasa na cefanar da filayen makarantu.
Dr Aikawa ya bada misali da makarantu irinsu Kwalejin fasaha ta Kano, da Kwalejin koyon Shari’a ta Aminu Kano da makarantar Firamare ta gidan sarki da Gouron Dutse da sauransu.
Gamayyar kungiyoyin data kunshin dukkanin manyan makarantu mallakar jihar Kano, sunyi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf daya samar da wasu dokoki dazasu hana cigaba da shiga filayen makarantu anan gaba.
Kungiyoyin dalibai daga dukkanin Manyan makarantun sun nuna goyon bayan Malaman nasu.
Gamayyar kungiyoyin masu ruwa da tsaki kan Ilimi ta yaba da matakin Gwamnatin Kano na rushe gine gine da akayi a makarantu
Date: