Thursday, April 30, 2026
HomeSiyasaGanduje ya caccaki Kwankwaso

Ganduje ya caccaki Kwankwaso

Date:

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje, yayi wasu kalamai na suka da ake zargin yayi sune akan tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon Gwamnan na kano, ya ambaci wani datakarar shugaban kasa a zaben daya gabata da cewar ya maida Jam’iyyar sa wata hanyar samun kudaden shiga tun bayan daya gaza samun biyan bukatar neman shugabancin kasar nan.

Ganduje ya kwatanta shi da wanda yazama dantakarar shugaban kasa sama ta ka, ta hanyar karbe iko da wata Jam’iyya bayan daya rasa Jam’iyya.

Dr Ganduje yayi wannan suka ne lokacin daya karbi bakuncin wadanda sukayi takarar shugabancin kasa a zaben daya gabata na jam’iyyu hudu a ofishinsa.

Jam’iyyun dai sun hadarda APP, NRM, APGA, da kuma ADP.

Ganduje yacigaba da cewa, tun bayan da dantakarar shugaban kasar ya fuskanci bazai kaiga nasara ba, sai yayi kokarin maida Jam’iyyar wata hanyar samun kudaden shiga, inda har takaiga ya Kori wanda yasamar da Jam’iyyar, amma dai bazai nasara ba, acewar Ganduje.

Maganganun na Ganduje dai wadanda yayisu batareda kama suna ba, ana zargin yayi sune ga tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya.

Alaka dai tayi tsami tsakanin tsoffin gwamnonin biyu kasa da shekara biyu bayanda Dr Abdullahi Umar Ganduje yazama Gwamnan kano.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories