Wednesday, August 26, 2026
HomeLafiyaGwamnatin Jihar Kano Bazata Lamunci Sayarda Jabun Magunguna ba~ Pharmacist Ghali

Gwamnatin Jihar Kano Bazata Lamunci Sayarda Jabun Magunguna ba~ Pharmacist Ghali

Date:

Gwamnatin Jihar Kano bazata lamunci Sayarda Jabun Magunguna ba

Gwamnatin Jihar Kano tace bazata lamunci dillanci dama Sayarda Jabun Magunguna a fadin jihar ba.

Darakta Janar na hukumar samarda magunguna da sauran kayayyakin lafiya ta jihar Kano Pharmacist Ghali Sule shine yabayyana hakan lokacin dayake ganawa da manema labarai.

Pharmacist Ghali yace, shirye shirye sunyi nisa wajen kaddamar da wani kwamiti da zai dauki gabarar tantancewa da sanya idanu akan masu sayarwa da shigo da magunguna da sauran abubuwa masu alaka domin kaucewa sayarda baragurbin magani a cikin al’umma.

“Gwamnatin Kano karkashin kwamishinan Ma’aikatar lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf, ta kafa wani kwamiti na masau ruwa da tsaki wanda zai fara aiki nan bada jimawa ba, aikin kwamitin shine tantance ayyukan dilolin magunguna da sauran masu sana’o’i dake da alaka domin tsaftace harkar” cewar Pharmacist Ghali Sule.

Kodayake acewar Pharmacist Sule, sanda yakarbi aikin jagorancin hukumar ya tarar da bashin sama da Naira Biliyan daya, amma duk da haka gwiwar su batayi sanyi ba wajen cigaba da gudanar da ayyukan suba.

“A lokacin da mukazo mun tarar da bashin Naira Biliyan daya da Miliyan 200 wanda ‘Yankwangila ke bi, amma bayan zama da mukayi dasu mun fito da tsarin biyansu bashin cikin watanni 12, kaga Naira miliyan 100 kenan duk wata” inji Pharmacist Sule.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories