Gwamnatin Jihar Kano taja kunnen Ganduje akan shigowa Kano
Gwamnatin jihar Kano tace bazata lamunci duk wani yunkuri na tada zaune tsaye, tare da kawo matsala ga zaman lafiyar da al’ummar jihar ke mora ba.
Kwamishinan ma’akatar ilimi ta jihar kano Hon Umar Haruna Doguwa shi ne ya bayyana hakan awani taron manema labarai da ya gudanar a safiyar talata.
Hon Doguwa yace, bayanan sirri sun nuna cewa tsohon Gwamnan Jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na shirin shigowa domin yin gangami a ranar alhamis, wadda kuma ranace da Gwamnatin Kanon ta tsara domin bayar da tallafi ga matasa.
Kwamishina Doguwa ya cigaba da cewa, Gwamnatin kano ta tanadarwa al’ummar Jihar ayyukan raya kasa da bunkasa tattalin arziki, wanda hakan zai kara janyo hankalin masu zuba jari daga sassan duniya domin shigowa jihar kano.
Yace, ba kuma zasu amince da wasu su rika cin mutunci da zagin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shatima ba a matsayinsu na iyayen kasa
Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da kotun koli ta tabbatarwa Gwamna Abba Kabir Yusuf nasara a shari’ar da Jam’iyyar APC da dantakarar ta Dr Nasiru Yusuf gawuna suka kalubalanci nasarar da jam’iyyar NNPP da Gwamna Abba suka samu a zaben da akayi awatan maris din shekarar da ta gabata.