Gwamnatin jihar Kano zata cigaba dakai ‘yan asalin jihar karatu kasashen waje…
Awani bangare na cika alkawuran data dauka lokacin yakin neman zabe na baiwa bangaren ilimi muhimmanci, gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf ta baiwa ofishin sakataren gwamnatin jihar daya fara aiwatar da shirye shiryen tantance ‘yan asalin kano domin daukar nauyin karo karatu a kasashen waje.
Acikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnatin tace wannan dorawa ne akan Shirin da gwamnatin kano karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tayi a shekarar 2015 na daukar nauyin daliban Kano masu digiri mai daraja ta farko 503 domin cigaba da karatunsu a kasashe akalla 14.
Sanarwar ta Kara da cewa ” la’akari da wannan mataki, ana gayyatar duk wadanda suka dace dasu aike da takardunsu domin karo karatu a shekarar karatu ta 2023/2024.
Duk wanda yake son morar wannan tsari dole yakasance dan asalin kano Kuma Wanda keda digiri mai daraja ta daya ko mai kama dashi, sannan yakasance me lafiya.”
Sanarwar ta cigaba da cewa, duk wadanda suka cika ka’idojin sai su aike da takardunsu ta adireshin yanar gizo www.kanostategov.ng. kafin daga bisani agayyacesu domin tantancewa.
Gwamnatin jihar Kano zata cigaba dakai ‘yan asalin jihar karatu kasashen waje… Gwamna Yusuf
Date: