Gwamnatin Jihar Kano ta ce a shirye take wajen goyon bayan duk wani tsari da zai taimakawa matasa maza da mata.
Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano Baba Halilu Dantiye shine yabayyana hakan yayin dayake jawabi lokacin kaddamar da shirin TEENSMATA na wayarda kan matasa maza da mata akan yadda zasu inganta rayuwarsu, Shirin dake samun tallafin USAID.
Datake Karin haske kan yadda Shirin yake, wakiliyar Hukumar ta USAID kuma Darakta a kungiyar Yellow Brick, Madam Carroll Ofom Somorin, tace an zabi jihohi biyune a Najeriya Legas da Kano domin aiwatar da Shirin a matakin gwaji, a Jihar kanon, an dauki kananan hukumomin Ungogo da Wudil.
A jawabinsa tunda fari Wakilin hakimin Ungogo Alh Shehu Abdulkadir, ya yabawa wannan shirin inda yace zasu cigaba da baiwa Shirin goyon baya a dukkanin matakai.
Taron ya samu halartar wakilan ma’aikatun Lafiya da matasa da wasanni da kuma ma’aikatar Mata, sai kungiyoyi masu zaman kansu dake yaki da shaye shayen miyagun kwayoyi tsakanin matasa.