Thursday, April 30, 2026
HomeMuhalliGwamnatin Kano ta ƙaddamar da feshin maganin sauro a asibitoci

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da feshin maganin sauro a asibitoci

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana zazzabin cizon sauro a matsayin daya daga cikin cututtukan data Sanya a gaba domin fatattakarsa a tsakanin al’ummar jihar nan.

Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ambassador Alhaji Ahmadu Haruna Zago shine ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da aikin feshin maganin sauro a asibitin Gwagwarwa.

Cikin wata takarda da aka rabawa manema labarai mai dauke dasa hannun Jami’in yada labaran hukumar Kamal Umar Kurna, Shugaban yace aikin feshin maganin rahotanni sun bayyana cewa an shafe kusan shekaru 8 ba’a yi shi ba a asibitoci da unguwannin jihar nan, a dan haka akwai bukatar al’umma su cigaba da karfafa yunkurin gwamnati wajen inganta rayuwarsu.

Wasu daga cikin marasa lafiyar da muka tattauna dasu sun bayyana cewa da yawan majinyata a asibitocin gwamnati a yanzu suna kwasar cutar cizon sauro ne a asibitocin maimaikon Sama musu lafiya.

Asibitocin da aka fara gudanar da aikin feshin maganin sauron a yau sun Hadar da asibitin Sir Sunusi da Asibitin Gwagwarwa sai Kuma Asibitin waziri gidado dake unguwar Bachirawa.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories